Ministan shari’a na kasa, Malami Abubakar, ya bada umurnin hukunta duk wanda aka kama da take dokar haramta Twitter ta hanyar anfani da barauniyar hanya.
Kakakin ministan, Umar Gwandu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ministan ya fitar.
Wannan dai yana zuwa ne biyo bayan haramta anfani da Twitter a Najeriya da gwamnati ta yi, ranar Juma’a.
To sai dai, duk da yanke shafin da kanfanonin sadarwa su ka yi bayan samun umurni daga gwamnati, dayawan ‘yan Najeriya, sun bijerewa umurnin inda su ke ci gaba da anfani da shafin Twitter ta barauniyar hanya.
“Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya ba da umurnin hukunta duk wanda aka kama yana anfani da Twitter ta barauniyar hanya a Najeriya,” a cikin sanarwar.
Haka kuma, ministan, ya umurci ofishin hukunta masu laifi na kasa da su hada hannu da Hukumar sadarwa ta kasa domin zakulo masu keta dokar tare da hukunta su ba tare da bata lokaci ba.
Haramta anfani da Twitter dai na zuwa ne bayan da kanfanin ya goge sakon Buhari da ya yi a kan yan aware na BIAFRA, kan abinda kanfanin ya kira da taka doka.
Gwamnatin buhari bata dauki lamarin da sauki ba inda cikin wata sanarwa ta tabbatar da haramta amfani da manhajar tuwita a duk fadin kasar ta najeriya mai yawan adadin muitane da ya kai sama da miliyan dari biyu da hamsin.
Amma sai dai ana iya cewa dokar haramta tuwita din ta bar baya da kura domin an jiyo masu amfani da manhajar tuwita a najeriya na bayyana koken su dangane da al’amari, inda da dama suka samarwa da kawunan su mafita inda suka rungumi wasu hanyoyin dabaru nna amfani da canjin muhalli domin aiwatar da sabgogin su a wannan dandali na tuwita.
Sai dai gwamnatin ta buhari tayi barazanar kama duk wadanda sukayi kunnen uwar shegu da umarnin.