A halin da ake ciki Gwamnatin tarayya tana kan ganawa da wakilan kungiyar Kwadago ta TUC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ganawar da suka fara da karfe 5 na yammaci, ana sa ran za su tattauna Gwamnatin ne dangane halin da ake ciki na irin mawuyacin hali sakamakon cire tallafin Mai.
Idan za tuna dai a ranar Larabar da ta gabata hadakar kungiyoyin Kwadago da suka kunshi NLC da TUC sun gudanar da wani zama tare da Gwamnatin tarayya amma an tashi zaman baram-baram.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ke jagorantar tawagar Gwamnatin tarayyan a wajen zaman.
Sauran tawagar sun kunshi gwamman babban Bankin kasa (CBN), Godwin Emefie; tsohon gwamnan Jihar Edo, Comrade Adams Oshiomhole; da babban jami’in gudanarwa na kamfanin Mai ya kasa (NNPCL), Mele Kyari.
Sauran da suka halarci zaman sun hada da babban Sakataren (NSDC), Zacch Adedeji; mataimakin shugaban na NNPCL, Yemi Adetunji; tsohon kwamishinan yada labaran jihar Legas, Mr Dele Alake; Hon James Faleke, da wasu.
Shugaban TUC na kasa, Festus Osifo ne ya jagoranci tawagar bangarensu a yayin ganawar.
Karin bayani daga baya:
A wani labarin na daban gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da korar jami’an cibiyoyi masu kula da harkokin Hajji a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamnan ya kuma nada jami’an rikon kwarya da za su rika lura da yadda ake gudanar da ayyukan hajjin na shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya bayyana abubuwan da ake bukata jami’an wucin gadin da aka nada da su fara aiki cikin gaggawa don sauke alhakin da ke kansu.
Sanarwar ta kuma umurci sabbin jami’an cibiyar da aka nada da su yi gaggawar ganawa da babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da aka nada kwanan nan domin gudanar da taron gaggawa a ranar Lahadi 4 ga watan Yuni 2023 a hedkwatar hukumar.
Wannan matakin na zuwa ne, a wani yunkuri na yin gyara da kuma daidaita harkokin tafiyar da al’amuran hukumar aikin Hajji a jihar wanda sabuwargwamnatin jihar ta kuduri aniya.