Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe fiye da Naira biliyan daya ga Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) Wudil domin biyan kudaden alawus na ma’aikatan jami’o’in.
Kwamishinan ilimi na manyan Makarantun jihar, Dakta Yusuf Ibrahim Kofarmata ne ya bayyana hakan a yayin taron hadin gwiwa karo na 3 da shugabannin manyan makarantu, hukumar bayar da tallafin karatu, da manyan ma’aikatar jami’o’in suka gabatar wanda aka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano.
Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba.
Gwamnan Kebbi Ya Rantsar Da Sabon Babban Alkali Da Shugabannin Manyan Makarantun Jihar
Ya ce, gwamnan ya amince da Naira miliyan 279 ga jami’ar YUMSUK don biyan alawus da kuma karin Naira miliyan 66 don yin taron yaye Dalibai na jami’ar.
Hakazalika, ADUSTECH, ta samu kason kudi fiye da Naira miliyan 629 domin biyan ma’aikatan kudin karin aiki da kuma Naira miliyan 38 na alawus ga Malaman jami’ar.
A wani labarin na daban gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sauke babban basarake kuma Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, Alhaji Abdulrazak Isa Koto, tare da wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Bello ya bayyana Alhaji Ahmed Tijani Anaje, wanda shi ne OHI na OKENWE a matsayin sabon Ohinoyi na Ebiraland.
An sanar da sauke Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, wanda kuma shi ne shugaban majalisar gargajiya ta Lokoja/Kogi a ranar Litinin a taron majalisar zartaswa ta jihar da aka gudanar a dakin taro na Exco na gidan https://nigeria21.com/hau da ke Lokoja.
Gwamna Bello a lokacin da yake sanar da sauke sarakunan, ya ce, “Bayan bin dokokin da suka kafa masarautun gargajiya, da dokoki da ka’idojin da suka dace, mun cimma matsaya kamar haka:
“An sauke Mai Martaba, Alhaji Abdulrazaq Isah Koto, Ohimege-Igu Koton-Karfe, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Gargajiya ta Karamar Hukumar Lokoja/Kogi, an mai da shi zuwa Karamar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.
“An sauke Mai Martaba, Sam Bola Ojoa, Olu Magongo na Magongo, an mai da shi zuwa garin Salka, karamar hukumar Magama ta Jihar Neja.
“An sauke mai martaba, Samuel Adayi Onimisi, Obobanyi na Emani, an mai da shi zuwa Doko, karamar hukumar Lavun ta jihar Neja.”
Source: LEADERSHIPHAUSA