Gwamnatin Kaduna Na Ci Gaba Da Rusa Muhallai Na Yan Musulmi Mabiya Shekh Zakzaky A Najeriya
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, a cigaba da rushe-rushen da gwamnatin jihar Kaduna take yi a kan muhallan ƴan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H), da misalin ƙarfe uku da wani abug na daren Lahadi wayewar garin yau Litinin ne yaran gwamna Nasiru El-rufa’i suka rusa Fudiyya Maraban Jos.
Bayan rushewar da suka yi wa Fudiyyar kuma, sai suka afkawa ƴan uwan da suke wajen da barkonon tsohuwa da kuma harsasai masu rai.
Sun yi harbi ne sosai na kan-mai-uwa-da-wabi akan ƴan uwa da ma mutanen garin da suka fito ganin me yake faruwa.
Amma duk da ruwan harsasan da suka yi Allah bai basu sa’ar samun ko mutum daya ba.
Jami’an tsaron sun dai yi ƙoƙarin kwashe kwanson harsasan da na barkonon tsohuwar da suka harba, amma dai bayan tafiyarsu mun samu ɗaukar hoton wasu daga ciki da kuma wuraren da suka huhhuda da harbi.
Idan ba a manta ba dai, dama wata takarda ta fita a kwanakin baya na irin ɓarnar da suka shirya yi a muhallan IMN wanda suke nufin muhallan harka Islamiyya ƙarƙashin jagorancin Sayyid Zakzaky (H).
Wakilanmu sun ji mutanen gari dai suna Allah wadai da abinda jami’an tsaron suka yi.