Gwamnatin Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta kashe wajen ingantawa da habaka ayyukan hukumar ‘yan sanda.
Gwamnatin Buhari ta ce, a cikin shekaru kasa da uku, ta kashe sama da Naira biliyan wajen gyara da habaka ofisoshin ‘yan sanda.
Gwamnatin Buhari ta sha bayyana aniyarta na samar da wadatattun kayan aiki ga hukumar ‘yan sanda.
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta bayyana cewa, ta kashe akalla Naira biliyan 5 wajen gyara ofisoshin ‘yan sanda da barikin soja a fadin kasar nan tsakanin 2019 zuwa 2022.
Hakazalika, gwamnatin ta ce ta yi ingantayya ga wasu wuraren horon jami’ai da cibiyoyi, ciki har da gyaran gine-gine da samar da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.
Wannan batu na fitowa ne daga bakin ministan harkokin ‘yan sanda na Najeriya, Maigari Dingyadi yayin da yake tsokaci game da tasirin gwamnatin Buhari daga 2015 zuwa 2023.
Wuraren da hukumar ta gyara Dingyadi ya kuma bayyana wasu daga cikin barikin soja da aka gyara da suka hada da na Kebbi, Edo, Borno, Yobe, Gombe, Bauchi, Plateau, Abia, Bayelsa, Nasarawa, Niger, Sokoto, Ogun, Lagos da babban birnin tarayya Abuja.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, gwamnati ta kashe wa rundunar ‘yan sandan Abuja N1.3bn, ta gyara makarantar ‘yan sanda dake Enugu a kan kudi N1.2bn da kuma kafa sabon sashen kiyaye manyan laifukan yanar gizo.
Ta ina aka samu kudaden wadannan ayyukan? Ya bayyana cewa, ayyukan da aka yi an yi su ne ta hanyar asusun tallafin hukumar ‘yan sanda ta Najeriya, This Day ta ruwaito.
Hakazalika, ya bayyana nasarori da hukumar ta samu wajen habaka manhajar horo ga cibiyoyin horo da karantarwa na hukumar.
A bangare gudan, gwamnatin shugaba Buhari ta sha bayyana manufar inganta ayyukan hukumar ‘yan sanda ta hanyar ba jami’ai horo mai inganci.
An gurfanar da ‘yan APC da PDP 14 a Borno bisa aikata wani babban laifi
A wani labarin kumwa, rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta gurfanar da wasu mutum 14 da ake kyautata zaton suna son tada zaune tsaye a jihar.
Wadanda aka gurfanar din sun hada da mambobin APC 12 da kuma na PDP biyu yayin da aka samu hargitsi a wurin kamfen.
Wannan ya faru ne jim kadan bayan da aka farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa na PDP, Aiku Abubakar a jihar.