Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa (NSA), Babagana Monguno, ya ba da umarnin tarwatsa duk wasu haramtattun rundunonin tsaron da ke gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba kuma ba da umarnin Gwamnati ba, a duk fadin Nijeriya.
Shugaban sadarwa a ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaron (ONSA), Zakari Usman, ya yi bayanin haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya kuma yi gargadi game da amfani da wadannan rundunoni don karbar kudi, muzgunawa da tsoratar da ‘Yan Nijeriya.
Mai ba da shawarar ya gargadi mutane, kungiyoyi da abokan hulda na kasashen waje kan ayyukan wata kungiyar tsaro mai suna NATFORCE, wanda ya ce, an kafa ta ba bisa ka’ida ba a matsayin rundunar yaki da shigowa da manyan makamai, alburusai da kuma kananan makamai cikin Nijeriya.
Usman ya ce, “cibiyar kula da kananan makamai (NCCSALW) da aka gina a Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ita kadai ce cibiyar da Gwamnati ta kafa don kula da yaduwar kananan da manyan makamai a Nijeriya.”
“Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ya lura tare da bayyana damuwa game da yaduwar kakkafa rundunonin tsaro ba bisa doka ba a cikin kasar. Wadannan rundunonin sun kasance suna boyewa suna kuma aiki a matsayin wani bangare na tsarin tsaro na Nijeriya yayin da suke karbar cin hanci, cin zarafi da tsoratar da ‘Yan Nijeriya,” in ji shi.
daya daga cikin irin wadannan kungiyoyin ita ce NATFORCE, wanda ke kokarin yakar shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, da alburusai, da makamai masu guba da kuma lalata bututun mai, kuma ta shiga cikin sanya shingaye ba bisa ka’ida ba, da gudanar da bincike ba bisa ka’ida ba, kamewa da daukar mutane aiki.
“Don kauce wa shakku, jama’a da duk masu ruwa da tsaki su lura cewa NATFORCE haramtacciyar cibiya ce ba tare da wani umarni ko hukuma na gudanar da wadannan ayyukan ba. Wannan dabi’ar ba abar yarda ba ce, kuma ana gargadin masu tallata NATFORCE da su rusa shirye-shiryensu da ayyukansu nan take,” in ji shi.
Ya ce, “biyo bayan kafa cibiyar kula da yaduwar makamai a ranar 3 ga Mayun 2021, Nijeriya ta fara aiwatar da cikakken aiwatar da mataki na 24 na yarjejeniyar ECOWAS kan hana yaduwar kananan makamai. Dangane da wannan, ana karfafa masu ruwa da tsaki na kasa da kasa su yi aiki tare da cibiyar don karfafa manufofin Gwamnati da kungiyoyin jama’a.” In ji sanarwar.