Gobara ta tashi a wani sashen babbar kasuwar Onitsha, da ke a jihar Anambra, sai dai, ba a tabbatar da abinda ya haddasa ta ba.
Wannan iftila’in gobara da ya auku a tsakar daren jiya lahadi, wani dan kasuwa a kasuwar mai suna Obenta Jude ya ce, wasu shaguna biyu sun kone a wani sashe na kasuwar da akafi sani da titin Kano.
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4 Sun Kwato Alburusai
A Kaduna
Jude ya kara da cewa, jami’an kashe gobara sun zo kasuwar, inda suka kashe gobarar.
Shugabar hukumar kashe gobara na jihar Injiniya Martin Agbili ya tabbatar da aukuwar ifitila’in, inda ya ce, hukumar ta yi gaggawar tura Jami’anta zuwa kasuwar don kashe gobarar.
A cewar Shugabar hukumar, da kimanin karfe 2.20 na daren jiya ne hukumar ta samu labarin tashin gobarar bayan kiran wayar a kawo dauki, inda ya kara da cewa, hukumar ta tura jami’anta don su kashe gobarar.
A wani labarin na daban a yau ne kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta amince da takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Bashir Sheriff Machina.
Kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke tun da farko wadda ta bayyana Bashir Machina a matsayin halastaccen dan takarar sanatan APC a Yobe ta Arewa.
Bugu da kari kuma, kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar kan rashin amincewar da ta sanya daukaka karar.
Shugabar Kotun, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem wadda ta yanke hukuncin, ta ce babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yi gaskiya bisa tabbatar da zaben fidda gwani na majalisar dattawa wanda jam’iyyar APC ta gudanar ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata, wanda ya bai wa Hon. Machina nasara tare da bai wa hukumar INEC ta sanya masa ido wajen aiwatar dashi.
Idan dai za a iya tunawa jam’iyyar APC mai mulki ta garzaya kotun daukaka kara tare da neman ayi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke kana da bukatr a bayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar a Yobe ta Arewa.
Source:Legithausa