Gobara ta lalata kadarorin miliyoyin Naira, tare da kone matsugunin mutane sama da 120 a jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:08 na safe, a cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin a ranar Litinin.
Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
Ya ce hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara ta kai dauki inda gobarar ta tashi a Megida Onikanhun da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu ta jihar.
“Ma’aikatan kashe gobara, da isowar su, sun gano gaba dayan kasuwar da Edun ta kone.
Hukumar kashe gobara ta tarayya da sauran jami’an tsaro sun kai dauki wajen da gobarar ta tashi a jihar.
Darakta, Hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kasance masu sanya ido wajen amfani da kayan wuta.
Kazalika ya bukaci jami’an hukumar kashe gobara da suke kai dauki a lokacin da aka kira su don tabbatar da ceton rayuka da dukiyoyin al’umma.
A wani labarin na daban gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ce, gwamnatinsa za ta kafa gidauniyar tattara kudade domin biyan bukatun iyalan jaruman da suka rasu a bakin aiki.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bikin ranar tunawa da sojojin Nijeriya na shekarar 2024 da aka yi ranar Litinin a Kano.
Ya ce, gwamnatinsa za ta gayyaci manyan mutane a jihar domin su mara wa gwamnati baya wajen kafa gidauniyar tallafawan.
A cewarsa, za kuma a yi amfani da gidauniyar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da samar da ayyukan yi ga matasa.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa, Jiharmu ta dore da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma gwamnatinmu ba za ta bar komai a baya ba don aiwatar da wannan kyakkyawar aniyar,” in ji shi.
Da yake jawabi kan iyalan jaruman sojojin da suka rasu, gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen kyautata rayuwarsu.
Ya kuma bayyana cewa, iyalan jaruman da suka rasu, za su ci gajiyar tallafin da za a raba wa al’ummar jihar.
Gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Source: LEADERSHIPHAUS