A Najeriya ,akalla fursunoni uku ne suka gudun daga wani gidan yari da ake tsare da su a Illori dake jihar Kwara a tsakiyar kasar.
Sai yayin ganawa da manema labarai,Francis Enobore kakkakin hukumar dake kula da gidajen yari ,ya na mai bayyana cewa bincike na tafiya kam don tattance hanyoyin da mutanen suka yi amfani da su wajen tserewa daga inda ake tsare da su.Wannan ba shine karo na farko da ake fuskantar irin wadanan matsalloli daga gidajen yari a Najeriya.
A wani labarin na daban Sojoji 6 da mayaka masu ikirarin jihadi akalla 22 ne suka mutu, yayin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Najeriya da na Nijar da kuma ‘yan ta’addan gefe guda, a Yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ta MNJTF ta kara da cewar dakarun ta da suka kwanta dama yayin fafatawar ta baya bayan nan sun hada da sojojin Najeriya 4 da na Nijar 2, yayin da wasu 23 suka jikkata, a lokacin farmakin da suka kawo karshensa a ranar Talatar da ta gabata.
Tarihi dai ya nuna cewar tun shekarar 1994 aka kafa ginshikin farko na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF, inda a waccan lokacin ta kunshi sojojin Najeriya kawai, wadanda aka dorawa alhakin murkushe barazanar tsaro ta barayin shanu akan iyakokin kasar daga bangaren arewacinta.