Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tashar Ruwa ta Tudu acikin Karamar Hukumar Funtuwa ta jihar Katsina.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya wakilci shugaba Tinubu a yayin gudanar da bikin kaddamar da Tashar a ranar Alhamis.
Akume ya ce, gwamnatin tarayya ta kafa tashar Ruwa ta Tudu ne (Dry Inland Port ) a Funtuwa domin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya.
Sanata Akume ya bayyana jihar Katsina da yankin Funtuwa a matsayin yankin noma mai dimbin albarka wanda zai amfana da tashar Ruwan ta Tudu.
Ya kara da cewa, tashar za ta samar da ayyukan hawa da sauke kaya ga ‘yan kasuwa a Arewa ciki har da wasu kasashen Afirka, kamar Jamhuriyar Nijar.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya yabawa gwamnatin tarayya bisa yadda ta samar da tashar Ruwa ta Tudu a Funtuwa cikin jihar, Katsina.
DUBA NAN: Jam’iyyar APC Tazo Ne Domin Talakawan Adamawa
Tun da farko, Ministan ma’aikatar Ruwa da tattalin arziki, Adegboyega Oyetola ya ce, manufar kafa tashar Ruwa ta Tudu ita ce, rage cunkoso a tashar Ruwa, inda ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta fara gyara tare da inganta tashar domin gudanar da aiki cikin sauki.