Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya jaddada kira da yin hakuri da juriya a tsakanin daukacin kabilun Nijeriya a wannan lokaci na gudanar da watan Ramadana, da kuma bin tsarin dokokin da ke tabbatar da zaman lafiyar al’umma.
DUBA NAN: Hukumar Tace Fina Finai A Kano Ta Rufe Gidajen Gala
Cikin sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan Humwashi Wonosikou, ya rattabawa hannu, ta ce yanzu da al’ummar Musulmi a fadin duniya su ka fara gudanar da Azumin watan Ramadan na shekarar 2024.
“Gwamna Fintiri ya bukaci al’umma da su sanya tsoron Allah a cikin dukkan al’amuransu tare da addu’ar Allah ya yi amfani da watan na Ramadan ya kawo mana karshen tashe-tashen hankula da munanan abubuwan da ake gani a wasu sassan kasar nan, ina kira cewa yanzu lokaci ne na kauracewa munanan dabi’u da sauya su kyawawan halaye” Cewar sanarwar.
Gwamna Fintiri ya yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake nuna wa al’ummar Musulmi wannan wata na Azumin Ramadan, ya yi addu’ar samun nasarar azumin, ya ce, “Idan Musulmi ya yi azumi, sai ya tausaya wa ‘yan uwansa musulmi”.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “bayan kammala Azumin watan Ramadan, kasancewar lokaci ne na kame baki, ya kuma zama lokacin nisantar abubuwan da su ka haramta.
“Ramadan yana da fa’idodi da yawa domin makaranta ce da kuma lolaci ne na kawar da jahilci ta hanyar sauraron wa’azi da yin amfani da shi don magance matsalolin al’umma” Cewar gwamna.
A wani labarin na daban kwamitin Hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda (PCRC), ya zabi sabbin Shugabannin gudanarwa za su jagoranci kwamitin a jihar Adamawa.
Da yake jawabi a bikin rantsar da sabbin shugabannin a Yola, shugaban kwamitin na kasa, Mogaji Ibraheem Olaniyan, ya nemi shugabannin da su yi aiki tukuru ta yadda jihar za ta zama abin koyi ga sauran jihohi.
Olaniyan, ya ya kuma yi kira ga shugabannin da su bi dukkan hanyoyin da su ka dace wajan ganin kwamitin ya kai ga mataki na gaba.
A jawabinsa, shugaban kwamitin na yankin jihohin Arewa maso gabas, Attah Mustapha, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben ba tare da hamayya ba, inda ya ce, kwamitin zai taimaka wa aikin ‘yansanda wajen ganin ya yi tasiri da samun nasara a jihar.
A nasa jawabin, zababben shugaban kwamitin PCRC na jihar Adamawa, Musa Bubakari Kamale, ya yi alkawarin yi wa kowane mamban kwamitin adalci da samar da daidaito tare da rokon addu’o’i daga mambobin domin samun nasara