Gwamnatin tarayya (FG) ta lashi takobin kin dage zabe mai karatowa saboda barazanar tsaro da ake hasashe a fadin kasa.
A cewar gwamnatin, babu gudu ba ja da baya, zabe zai gudana kamar yadda aka shirya, sannan tana sane game da yadda INEC ke aiki tukuru tare da hukumomin tsaro saboda zaben.
Hukumar zaben, da farko ta bayyana yadda za ta tabbatar ta bada tsaron ciki da waje don ganin an aiwatar da zaben yadda ya dace.
Gwamnatin tarayya ta cire batun yuwuwar dagewa ko soke zabe mai karatowa saboda rashin tsaro, jaridar TheCable ta rahoto. Bayan INEC Tayi Magana Kan Fasa Zabe,
Lai Muhammad, ministan FG yada labarai, yayi jawabi game da batun a ranar Talata a taron bayyana nasarorin da mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya samu tsakanin 2015 zuwa 2023 a Abuja.
Yayi martani ne game da rahotannin kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) take fuskantar babban kalubale na soke zabe saboda rashin tsaro.
Ministan ya ce babu wata barazana saboda masu ruwa da tsaki suna iya kokarinsu wajen tabbatar da an shirya zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a rumfunan zaben kasar nan.
“Gwamnatin tarayya na nan kan bakanta cewa za’a gudanar da zabe kamar yadda aka shirya. Kuma babu abun da ya faru da zai canja hakan.” – NAN ta yanko maganarsa.
“Muna sane cewa INEC na aiki tare da hukumomin tsaro don tabbatar da an gudanar da zabe cikin nasara a fadin kasar.
“Haka zalika, hukumomin tsaro sun cigaba da ba ‘yan Najeriya tabbacin yadda suke aiki tukuru don tabbatar da zaben ya gudana cikin lumana.”
Da farko dia INEC ta ce za ta tabbatar ta bada tsaron ciki da waje ga masu aikin zabe da kayayyakin zabe, jaridar The Guardian ta rahoto.
Yayin jawabi game da kayayyakin horarwa na tsaron zabe a ranar Litinin, Abdullahi Zuru, kwamishinan INEC kuma shugaban board of Electoral institute, ya ce Babagana Monguno, mai bada shawara kan tsaron kasa, ya bada tabbacin tabbatar da tsaro da walwala a gangamin zabe mai karatowa.
Ta yuwu a fasa ko a dage zaben 2023, INEC A wani labari na daban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da cewa tsaro na barazanar hana zabe mai zuwa.
Hukumar tace matukar tsaro bai inganta ba, za a iya sokewa ko dage zaben mai zuwa.
Source:LegitHausa