Kungiyar masu safarar mai da iskar gas dake Najeriya, ta yi hasashen cewar nan bada jimawa farashin man dizel ka iya kaiwa naira dubu daya da dari biyar.
Wannan gargadi dai ya zo ne a yayin da farashin litar man dizal din a Najeriyar ya kai naira 800.
Tuni hasashen ya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin zullumi, lura da halin da ake ciki na matsin rayuwa a kasar, sakamakon yadda farashin kayayyakin da ake sarrafawa a masana’antu Najeriya suka yi tashin gauron zabi.
Ahalin da ake ciki dai galibin gidajen man kasar sun daina sayar da man dizel saboda tsadar da yayi, duk kuwa da cewa dashi ne ake safarar man fetur zuwa sassan Najeriyar.
Wannan ce ta sanya shugaban kungiyar ta masu safarar mai da iskar gas a Najeriya Bannet Korie, gargadin cewa matsawar aka cigaba da tafiya a haka ba tare da daukar kwararan matakai ba lallai farashin ka iya kaiwa naira dubu 1,500.
A wani labarin na daban kasar Rasha ta ce ta haramtawa wasu Amurkawa 963 shiga kasarta ciki har da shugaban Amurka Joe Biden da sakataren harkokin wajensa Antony Blinken da kuma shugaban CIA William Burns.
Haramcin tafiye-tafiye na da dan tasiri, a wani bangare dake tabbatar da tsamin dangantakar Rasha da Amurka da kawayenta tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.
Wannan na zuwa ne yayin da Katafaren kamfanin makamashi na kasar Rasha Gazprom ya sanar da dakatar shigar da iskar gas zuwa makwabciyar kasar Finland saboda kin amincewa da biyan ta da kudin kasar ruble.
Moscow dai ta bukaci abokan cinikinta daga “kasashe da basa ga maciji – ciki harda kasashe membobin EU – da su rika biyan kudin cinikin iskar gas da Rubels dinta, domin kaucewa takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen Yamma suka kakaba mata bayan mamayar Ukraine.