Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya nemi gafara akan yadda ‘yan sandan kasar suka yi amfani da hayaki mai sa hawayen da ya wuce kima lokacin wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai tsakanin kungiyar Real Madrid da Liverpool a karshen mako.
Yayin da ya gurfana a gaban Majalisar Dattawa domin amsa tambayoyi akan korafe korafen da suka biyo bayan wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turan, ministan ya ce amfani da hayaki mai sa hawayen ya hana samun tirmitsitsi wajen shiga filin wasan, sai dai ya ce abin takaici hayakin ya yiwa kananan yara illa.
Saboda haka ministan wanda ya bayyana cewar akalla mutane sama da 110, 000 suka ziyarci filin wasan karshen, ya nemi gafara game da amfani da hayakin mai sa hawaye, yayin da ya ce za a hukunta jami’an ‘yan Sandan da suka harba hayakin.
Shugaban faransa Emmanuel Macron ya bukaci gudanar da bincike na hakika dangane da lamarin, lura da yadda ministan cikin gidan ke ci gaba da fuskantar tuhuma dangane da rawar da ‘yan Sanda suka taka.
Ministan ya ce akalla magoya bayan Liverpool 30,000 zuwa 40,000 suka je filin ba tare da tikitin shiga wasan ba.
A wani labarin na daban gwamnatin Kasar Chadi ta kafa dokar kar-ta-kwana akan karancin abinci a kasar, inda ta bukaci kasashen duniya da su kai mata dauki domin shawo kan matsalar.Wannan bukata na zuwa ne kwana guda kafin ganawar da za’ayi tsakanin shugaban kungiyar kasashen Afirka, Macky Sall tare da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow dangane da bukatar fitar da abinci daga Ukraine.
Wata sanarwar gwamnatin sojin Chadi da aka karanta ta kafar talabijin, tace sakamakon tabarbarewar al’amuran da suak shafi karanci abinci da halin da ake ciki a wannan shekarar da kuma fargabar halin da jama’ar kasar ke iya samun kan su, gwamnati ta kafa dokar ta baci akan karancin abincin.
Sanarwar tace gwamnati tayi kira ga masu bada agaji da kawayen ta na duniya da su taimaka wajen kai dauki ga jama’ar kasar da suke fuskantar karancin abincin.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar mutane miliyan 5 da rabi ke fuskantar karancin abinci a Chadi, alkaluman dake nuna sama da kashi daya bisa 3 na jama’ar kasar, kuma suna bukatar daukin gaggawa.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a watan Maris da ya gabata tace akalla mutane miliyan 2 da dubu 100 ke bukatar taimakon abinci na gaggawa a Chadi a wannan wata na Yuni.