Shahararren Lauya mai rajin kare hakkin Dan Adam Femi Falana ya kai karar Gwamnatocin tarayya dana Jihohi 36 kotu da sauran masu fada aji ta bangaren ilimi, a kan irin halin da yaran da basu zuwa makaranta suke ciki.
Karar wadda babban lauya kasa tare da abokiyarsa tun suna ‘yan yara kwararriya ce ta bangaren ilimi Hauwa Mustapha,a madadin kungiyar ‘Alliance on Surbibing COBID-19’ da ta hada tare da Ministan ilimi da hukumar kula da ilimin bai daya suna daga cikin wadanda aka yi karar.
Babban mai shari’a na kasa tare da manyan masu shari’a na Jihohi, Ministan Babban birnin tarayya Abuja suna daga cikin wadanda aka yi karar,an shiga da karar ne ta hannun Lauyarsu Mrs Funmi Falana (SAN).
Karar tana magana ne kan zargin da ake yi yadda aka kasa amfani da Naira bilyan 68 kudaden da aka warewa hukumar saboda samar da ilimi kyauta ga kowane yaro a Nijeriya.
Falana yana so ne wadanda aka yi karar da suka hada da gwamnatin tarayya, ma’ikatar ilimi hukumar ilimin bai daya, da dukkan Jihohi 36 saboda alhakin samar da ilimi kyauta ga dukkan yara wadanda suka isa shiga makaranta ya rataya a kansu ne.
Koda yake dai shi al’amarin yara wadanda basu zuwa makaranta wadanda ake sa ran sun kai miliyan 20 da dubu 200,000 idan aka yi la’akari da rahoton UNICEF da ba’a dade da fitarwa ba shi yasa aka dauki matakin zuwa kotun.
Karar an shigar da ita ne ranar 19 ga Janairu na shekarar 2024 a kotun tarayya da ke Legas inda aka bukaci kotun da ta yi bayani akan tuhumar wadanda aka kai karar.
“Ana dai son a gane ko wadanda aka kai karar alhakin samar da ilimin bai daya a dole, kuma kyauta ga kowane yaro dan asalin Nijeriya da ya kai shekarun shiga makaranta,kamar yadda sashe na 2 karamin sashe na (1) dokar da ta bada damar samar da ilimi dole kuma kyauta mai namba, LFN, 2004.
“Ko rashin yin aiki yadda doka ta bada dama ga wadanda aka yi karar su bada abin da bai gaza kashi 50 kudaden ayyukan da za ayi da hakan zai nuna suma sun nuna suna bayan ba kowane yaro dan Nijeriya ilimi kyauta abin da dole ne sai hakan ta kasance, a matsayin sun yi na’ama da lamarin.Ba karamin laifi bane wajen kin yin amfani ga dokar data bada dama wajen samar da ilimin bai daya kyauta kamar yadda dokar shekarar 2004 ta ilimi ta tanadar.
A karar da Femi Falana ya shigar akotun tarayya Legas ranar 26 ga watan Janairu 2024, babban lauyan yace rahoto ya fitar da shi wanda hukumar kula da al’amuran gaggawa na kananan yara karkashin majalisar dinkin duniya bada dadewa bane aka kiyasta da akwai yara a Nijeriya da suka kai milyan 20.2 da basu zuwa makaranta.
Falana ya ce rahoton ya nuna daya daga cikin yara uku ‘yan Nijeriya baya zuwa makaranta,bugu da kari kuma kasar ita tafi yawan yara wadanda basu zuwa makaranta a duniya.
Ya ce “Wanda aka yi karar na farko shi ne Ministan shari’a shi ne kuma na farko mai kula ana tursasa bin doka kamar yadda kotunan Nijeriya suka bukaci da ayi hakan.
“Wanda aka yi kara na biyu tsarin Mulki ya bashi damar aiwatar da tsare-tsaren ilimi a kowane bangare na ilimi cikin inganci a Nijeriya.
“Cikin jerin wadanda ake kara hukumar kula da ilimin bai daya shi ke da alhakin rabawa Jihohi kudade da sauran masu ruwa da tsaki da jagorancin aiwatar da tsarin hukumar a illahirin Nijeriya.
“Na 4 zuwa 40 sun hada da wadanda suke lura da al’amuran shari’a na Jihohi 36 na fadin Nijeriya.
“Cewar dokar data kafa hukumar ilimin bai daya da wasu abubuwa da aka kafa, 2004 (UBEA) tana samar da ilimi da ya zama dole ga dukkan yara ‘yan Nijeriya da suka kai shekarun shiga makarantar Firamare da karamar Sakandare a Nijeriya.”
Wadanda suka shigar da karar suna bukatar kotun da ta tilasta yin wadannan abubuwan saboda adalci.
Kamar yadda sashe na 2 karamin sashe na(1)bada dama ta dole a samar da ilmin Firamare da karamar Sakandare kyauta kamar yadda dokar ilimi da dokokin Nijeriya na shekarar 2004,wadanda ake karar doka ta basu damar bada ilimi kyauta da yake dole ga yara wadanda suka kai shekarar shiga makarantar Firamare da karamar Sakandare
Sashe na 11 karamin sashe na(1)ya bada dama ta samar da ilimi daga Firamare zuwa karamar Sakanadare kyauta wanda doka ta bada na cewar gwamnatin tarayya zata rika bada kashi wanda bai kasa da kashi 2 ba na kudaden shigar da take samu a gidauniyar ta ilimi kowace shekara.
Hakanan ma dokar ta sashe na 11 karamin sashe(2)na samar da ilimin Firamare zuwa karamar Sakandare kyauta Jihohi ma ana son kowace Jiha ta samar da abin da bai gaza kashi 50 ba na yawan kudaden da za a kashe na ayyukan da za ayi,kafin ta samu cancantar samun tallafin na gwamnatin tarayya a karkashin karamin sashe na 1(1) na sashen.
Hakanan ma idan aka samu kin amincewa ko su wadanda ake karar suka kasa samun Naira bilyan 68 na ilimin Firamare da karamar Sakandare na yara wadanda suka kai shekarar shigaa Nijeriya, abin da bai dace bane kuma ya sabawa sashe na 1 karamin sashe na dokar samar ilimi da ta zama dole ayi amfani da ita (2).
Akwai doka da ke ba da umarni na na wadanda ake karar daga na 4 zuwa na 40 su biya na su kason kafin su samu damar yin amfani da Naira bilyan 68 daga cikin asusun ajiya na ilmin bai daya da rahoton bin umarni cikin kwana30 lokacin da kotu zata yanke hukunci.
Akwai doka da take umarni wadanda aka yi kara na 4 zuwa na 40 su biya nasu kason domin su samu damar yin amfani da kudaden da aka ware na samar da ilimin bai daya, idan lokacin yin hakan ya yi.
Source: Source:LEADERSHIPHAUSA