Fadar shugaban kasa ta mayar da martani a kan kwamitin bincike da Gudaji Kazaure ke jagoranta.
Mai magana da yawun fadar Shuagban Kasa, Malam Garba Shehu ya ce Kwamitin da dan majalisar tarayyar ke jagoranta haramtacce ne kuma ba Shugaba Buhari bane ya kafa sa.
Gudaji Kazaure ya yi ikirarin cewa kwamitinsa ya gano dalolin miliyoyi na kudaden da ake caji daga ajiyewa da cire kudi a asusun banki.
Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi raddi a kan wani kwamiti da ake ikirarin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kafa sa domin gudanar da bincike a kan kudaden da za a yi caji na cirewa da ajiyar kudi a asusun banki.
Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai wanda shine shugaban kwamitin, ya zargi wasu hukumomi da binciken ya shafa da kokarin hana shi aiwatar da aikinsa tare da mika rahoton abun da ya bankado ga shugaban kasa Buhari.
Kamar yadda kwamitin da ke binciken cajin kudin tun daga 2013 har zuwa yau ya bayyana, ya ce ya gano cewa babban bankin CBN ya tara sama da naira tiriliyan 80, amma ya yi zargin an yi kane-kane a kan kudin. Da yake martani a kan lamarin, kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce ba za a ce maganar Gudaji Kazaure na kwamiti bane domin shi ya kafa abunsa sannan ya nada mambobi harda alkalin alkalai.
A hirarsa da BBC Hausa Shehu ya ce dan majalisar ya samu shugaban kasa ya nuna masa za su kwato kudaden kasa ne, kuma cewa duk wanda zai fada ma Buhari kudi zai kwato toh zai yi maraba da haka.
A takaice Garba Shehu ya musanta ikirarin cewa shugaban kasar ne ya kafa wannan kwamiti.
Ya ce babu yadda shugaban kasa zai kafa kwamiti a tsari na gwamnati sannan ya baiwa dan majalisa sakatare sannan ya kira alkalin alkalai ya nada shi mamba.
A cewarsa yin hakan tamkar an yi wa tsarin mulki karen tsaye ne.
Ya ce kwamitin haramtacce ne yana mai cewa: “Ba shi da hurumi a doka, wannan ne yasa shugaban kasa Buhari ya ce a ruguza shi, sannan a kafa sabo a karkashin minustan shari’a.”
Kakakin shugaban kasar ya kuma yi al’ajabin makuden kudaden da Gudaji kazaure ke ambata a jawabinsa na cewa an yi sama da fadi kan biliyoyin daloli.
Shehu ya ce: “Wannan zargi na tiriliyan 160 da yake cewa an batar, a ina kudaden suke? Tiriliyan 160 fa.”
A cewarsa idan aka tattara dukiyar bankunan kasar baki daya, ba su kai kaso daya cikin uku na kudaden ba.
A wani labari, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin sojoji a kan tsoma baki a harkokin siyasa gabannin babban zaben 2023.
Buhari ya ce babban aikin sojoji shine su kare rayuka da tabbatar da zabe na gaskiya cikin lumana.
Source:LegitHausa