Wani Lauya ya fadawa Muhammadu Buhari ya kawo karshen matsalar kashe-kashe inda yace dole a tsige shugaban kasa.
Saheed Akinola esq. ya ce gwamnatin tarayya ta gagara kawo zaman lafiya a kasar nan.
Akinola ya bukaci Majalisar Tarayya ta tsige Shugaban kasar idan ba a kawo sauyi ba A dalilin kashe-kashen mutane da garkuwa da mutanen da ake fama da shi a Najeriya, wani lauya ya fara kiran a tsige shugaba Muhammadu Buhari.
Saheed Akinola ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya su fara shirin tsige Mai girma Muhammadu Buhari saboda yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a kasar.
Wannan lauya mai rajin kare hakkin Bil Adama da ke zama a Legas, ya yi hira ta musamman da Legit.ng, inda ya ce abubuwa sun sukurkuce a halin yanzu.
A cewar Lauyan, abubuwa sun cabe, kuma da wuya su dawo daidai, ya ce bai kamata shugaban kwarai ya rika nuna kamar daidai abubuwa suke ta tafiya ba.
Akinola yake cewa dole shugaban kasar ya yi maganin matsalolin da ake fuskanta, ya daina tunanin cewa abubuwa za su dawo, su gyara kansu da kansu.
A lokacin da Muhammadu Buhari ya fito takarar shugaban kasa a 2015, mutane sun yi masa kyakkyawan zaton zai kawo gyara, a cewar Saheed Akinola.
Hakan ya sa jama’a suka mara masa baya, suka ba shi kuri’ar da ta kifar da gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan, ya ce amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Masanin shari’ar ya ce matsalar tsaro da matsin tattalin arzikin da ake fuskanta sun nuna cewa shugaban kasa da mutanensa sam ba su san inda su ka dosa ba.
“Rikon da shugaban kasa Buhari ya yi a kan kashe-kashe, garkuwa da mutane, da ta’adin da ake yi, ya kara jawo matsalar rikicin kabilanci a Najeriya.” Inji shi.
Akinola ya ce: “Buhari da jami’an tsaro suna neman agaji, muna sa ran ya sauka daga kujerarsa, ko ya kara dage wa, ya yi aiki, ko dole majalisar tarayya ta tsige shi.
” Mun ji labari cewa Majalisar wakilan tarayya za ta halasta noma da safarar wiwi a Najeriya.”
Mai magana da yawun majalisar wakilai, ya bayyana wannan a jiya. Hon. Benjamin Okezie Kalu ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da yayi jawabi kan amfani da damammakin da za a samu daga tabar wiwi a Najeriya.