Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya ta Northern Elders Forum ta bayyana cewa ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya ta bai wa ‘yan kabilar Ibo masu fafutukar kafa kasar Biafra damar ballewa cikin ruwan sanyi, maimakon kisan jama`a ‘Yan Arewa da ‘yan IPOB ke yi babu gaira babu dalili.
Mai magana da yawun kungiyar Dakta Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai.
A cewarsa, lokaci ya yi da Dattawan Arewa za su samo mafita a kan matsalolin da suka dakile ci gaban yankin baki daya.
Dakta Hakeem ya yi bayanin cewa bangaren Arewacin kasar ya san irin mawuyacin halin da ya shiga a lokacin yakin basasar da aka yi a baya, don haka yankin ba zai so a sake maimaitawa ba.
“An yi yaki kowa ya ji jiki. Idan suna son su balle kuma shugabanninsu sun goyi bayansu, ba wani dalilin yaki gara ma su balle domin ya fi zama alheri,” in ji shi
Ya kara da cewa babu wani shugaban Ibo da ya fito fili ya ce abin da suke yi na kashe-kashe da kone-kone su bari wanda ya nuna a cewarsa, “suna samun goyon bayan shugabanninsu.”
“Fitinar zamansu a Nijeriya ta ishe mu, idan gwamnati ba za ta dauki mataki ba to ta ba su dama a yi kuri’ar jin ra’ayi.” In Ji shi.
Kungiyar ta dattawan arewa na ganin fitinar da cigaba da zama da ‘yan biyafara zata haifar ba karama bace domin hakan suka yanke shawarar kira ga gwamnatin tarayya da ta barsu su balle cikin ruwan sanyi.