Kamfanin Dangote Industries Limited ya dauki hayar Lauya, an je babban kotun tarayya a Abuja.
Hakan na zuwa ne a sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin da babban kotun jiha tayi a Lokoja.
Dangote Industries Limited suna so a kammala saurarn korafinsu, kafin a karbi korafin gwamnati.
Kamfanin ya shigar da kara a kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja a kan sabaninsa da Gwamnatin jihar Kogi.
The Nation ta ce Lauyan Dangote Industries Limited yana so Alkali ya bada muhimmanci a shari’ar da ke gaban babban kotun jiha mai zama a Lokoja.
Ana shari’a tsakanin kamfanin Dangote da gwamnatin jihar Kogi a kan mallakar kamfanin simintin Obajana, wannan ya sa ake neman kotu ta raba gardama.
Abin da gwamnatin Kogi take so shi ne a soke yarjejeniyar da aka shiga tsakanin kamfanin simintin na Ajaokuta da Dangote a shekarar 2002 da kuma 2023.
Lauyoyin Dangote suna ganin babu dalilin da za ayi watsi da yarjejeniyar da aka bi doka wajen sa hannu, suka ce a dakata da maganar har a gama shari’a.
A hukuncin da ya zartar, Alkalin da ke sauraron karar, R. O. Ayoola ya yi watsi da bukatun lauyoyin Dangote, Paul Usoro (SAN) da Reuben Atabo (SAN).
Ayoola ya yarda da maganar Lauyan gwamnati, Abdulwahab Mohammed (SAN), ya ce zai fi kyau a saurari korafin Dangote tare da ainihin shari’ar da ake yi.
A kotun daukaka kara, Dangote ya bukaci a soke hukuncin da Mai shari’a R. O. Ayoola ya zartar, sannan kuma a saurari karan biyu a lokuta dabam-dabam.
Kamar yadda rahoton ya nuna, Lauyan da ya tsayawa kamfanin Dangote ya soki kotun a kan sauraron korafin gwamnatin Kogi tare da na shi korafin.
Kamfanin yana gardamar dokar kasa ta ce a saurari korafi ne daya bayan daya, kafin a kai ga wani.
Akasin abin da ake kokarin yi a wannan shari’ar a Kogi.
Sannan Lauyan da ya tsayawa Dangote Ltd yana zargin kotun da ke zama a Lokoja da kuskuren kammala sauraron korafinsa kafin a iya kai ga wani karar.
Rikici a LP a Taraba A Jihar Taraba, an ji labari Shugabannin Jam’iyyar Labour Party sun yi taro, a karshe aka sauke Shugabar Jam’iyya saboda zarginta da aikata wasu laifuffuka.
Esther Gulum ta ce zargin da ake yi mata na cin kudi da yi wa PDP aiki duk karya ne, ta ce cikakkiyar ‘yar Obidient ce ita kuma mai biyayya ga jam’iyyar LP.