Kungiyar daliban Najeriya ta nemi shugaba Buhari da ya gaggauta kawo karshen yajin aikin da malamai ke yi.
Malaman jami’a sun shiga yajin aiki tun watan Fabrairu, hakan ya kawo koma-baya ga fannin ilimin kasar.
Kungiyar daliban ta Najeriya (NANS) ta mika kokenta ga shugaban kasa manjo Muhammadu Buhari mai ritaya da ya yi hakuri ya kawo karshen yajin aikin malaman jami’a ASUU.
Daliban sun roki Buhari da ya daidaita da lakcarorin Najeriya domin ba su damar komawa makaratu su ci gaba da karatu.
Wannan batu na fitowa ne daga bakin shugaban NANS, Kwamared Usman Barambu a Abuja yayin zantawa da manema labarai, The Nation ta ruwaito.
An kai makura, daliban Najeriya sun roki Buhari ya yi hakuri ya kawo karshen yajin ASUU.
Barambu ya koka da cewa yajin aikin ya kassara fannoni daban-daban na ilimin jami’o’in gwamnati tare da kawo kari ga shekarun kammala karatu ga dalibai.
Shugaban fannin yarjejejiya na NANS, Usman Ayuba ya roki Buhari ya yi amfani da kwarewarsa da ikonsa wajen kawo karshen yajin.
Haka nan, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.
Ya kuma yi kira ga warware matsaloli da dama da suka addabi Najeriya, NewsPress ta tattaro. Idan baku manta ba, jami’o’in gwamnati a Najeriya sun kasance a garkame tun ranar 14 ga watan Fabrairu, lamari da ya kawo tsaiko ga ilimi a Najeriya.
Dalibai sun sha kokawa, kungiyar ASUU ta ki daga kafa kan bukatun da ta ba gwamnati saboda muhimmancinsu.
A wani labarin, hukumar gudanarwar jami’ar jihar Gombe (GSU) ta kira dukkan malaman ta bukaci dukkan ma’aikatanta dake hutun karatu da su gaggauta dawowa aiki.
Wannan na zuwa kira na zuwa ne a yau Litinin 5 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Magatakardar jami’ar, Dakta Abubakar Aliyu Bafeto, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Satumba 5, 2022, ya umurci malaman jami’ar da ke karatu a Najeriya da su koma bakin aiki kasancewar jami’ar ta dawo karatu.
Source: LEGITHAUSA