Rundunar dakarun sojin Najeriya ta ce ta ceto akalla mutane 30 daga hannun ‘yan ta’adda a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Rundunar dakarun Ta ce ta kwato mutanen ne daga hannun ‘yan kungiyar IS ta yammacin Afrika da Boko Haram, sakamakon samamen da take yi a kauyukan Ndufu da Musiri, da ke da nisan akalla kilomita 125 daga Maiduguri, babban birnin jihar,
A sanarwar da ta fitar a jiya Juma’a rundunar dakarun sojin na najeriya ta kafar sadarwar Twitter, rundunar sojin Najeriyar ta kuma ce ta kashe ‘yayan kungiyar ISWAP da Boko Haram da dama, tare da lalata sansanoninsu.
Ta kuma ce dakarunta sun gano dimbim makamaida ba a bayyana adadinsu ba daga hannun ‘yan ta’addan.
wani labarin na daban kuma AGwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da dokar zabe ta sherkarar 2022, amma fa za ta cire sashe na 84, karamin sashe na 12 wanda ya ce dole ne duk wani mai rike da mukamin gwamnati da ke da sha’awar yin takara a zaben kasar ya sauka daga mukaminsa.
Wannan sanarwar na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da wata kotu da ke zamanta a garin Umahia ta jihar Abia a kudu maso gabashin kasar ta umurci ministan shari’a na kasar, Abubakar Malami da ya cire sashen ba tare da bata lokaci ba.
Gwandu ya ce matakin da ma’aikatar shariar ta dauka, biyayya ce ga umarnin da kotu ta bayar a Juma’ar.