Labarai daga jihar kadunan najeriya na nuni da cewa yau 1 ga watan july 2021 za’a cigaba sa sauraron shari’ar jagoran mabiya darikar shi’a sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ake tsare dashi fiye da kwanaki dubu biyu.
Gwamnatin najeriya tana rike da shugaban na darikar shi’a a najeriya bisa zargin tarewa tsohon shugaban sojin najeriya hanya da ake zargin mabiya malamin sunyi.
Babbar kotu a Abuja ta jima da yanke hukuncin cewa, a saki malamin kuma buya shi diyyar naira miliyan hamsin sa’annan a gina masa gida duk jihar daya zaba domin a rushe gidan sa dake zariya tun a shekarar 2015 lokacin da sojojin najeriya karkashin jagorancin janaral tukur burutai suka kai hari gidan nasa.
Gwamnatin najeriya karkashin jagorancin shugaba muhammadu buhari ta kekasa kasa taki aiwatar da umarnin babbar kotu wacce mai shari’a kole wale yake jagoranta wacce kuma tayi umarnin a saki malam zakzaky kuma a biya shi diyyar naira miliyan hamsin.
Daga baya aka dawo aka soma sabuwar shari’a a karkashin jagorancin kaduna, sabuwar shari’ar wacce masana shari’a suka tabbatar da cewa bata kan ka’ida domin babbar kotu wacce take gaba da wannan ta yanke hukunci a kan wannan case din.
Daga wancan lokaci zuwa yanzu anyi zame zame da dama amma ba’a kai ga yanke hukunci ba zuwa yanzu sakamakon matsalolin da akayi ta fuskanta.
Wakilin mu daga kotun ta kaduna Barriter Ishaq Adam ya tabbatar mana da cewa yanzu haka suna kotu kuma alkalin kotun ya samu isowa amma zuwa yanzu ana jiran babbar lauya wanda ke kare malamin watau Barrister Femi Falana SAN, inda da zarar ya iso ake sa ran za’a cigaba da shari’ar.
Zamu kawo muku cigaban wannan shari’a da aka jima ana fafatawa kuma zamu kawo muku labarin yadda ta kaya bayan an kammala wannan shari’a wacce ta dauki hankulan mutane daga ciki dama wajen kasar najeriya