Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba ta (CDD), ta yi Allah-wadai da cin tarar Naira miliyan biyar da Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta yi ga gidan talabijin na Trust TV da wasu kafafen yada labarai uku, saboda watsa shirye-shiryen da suka shafi ‘yan ta’adda.
Haka nan NBC ta ci tarar kamfanin Multichoice Nigeria Limited, mamallakan DSTV, TelCom Satellite Limited (TSTV) da NTA-Startimes Limited, saboda watsa wani shiri da hukumar yada labarai ta BBC ta yi mai taken, ‘Bandits Warlords Of Zamfara’.
CDD, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar da Daraktarta, Idayat Hassan ta fitar, ta bayyana sanya tarar a matsayin abin zalunci, inda ta bukaci hukumar ta janye matakinta cikin gaggawa.
A cewar Hassan, tarar wani yunkuri ne na cin mutuncin kafafen yada labarai da kuma tauye hakkin ‘yan kasa na fadin albarkacin bakinsu da yada labarai.
A wani labarin na daban Dan takarar majalisar Dattawa na Kano ta tsakiya a inuwar jam’iyyar PDP, Dokta Abubakar Nuhu danburan ya bayyana cewa kudurinsa shi ne na Kano abubuwa wanda zai zama na ci gaba a Kano ta tsakiya domin duk abinda ya dami jihar Kano ya tattara ne a Kano ta tsakiya.
Ya yi nuni da cewa a Kano ta tsakiya ne ake da mafi yawancin yan kasuwa da malamai da kusan duka abubuwa da mutane ke bukata suke so su yi na rayuwa dan haka su yi abinda ya dace a wannan lokaci dan tura wakilci daya.
Ya ce dan majalisar Dattawa na yanzu na yankin, Wanda tsohon Gwamna ne me ya yi akan ilimi, da nemawa mutane abin yi dan haka mutumin da ya yi Gwamna kullum tunaninsa shi ne ya riga ya gama aikinsa zai yi wahala kaga ya iya daga hannu a majalisa ya kawo wani abu daya dami al’ummarsa ko yaje ofis mutum ya nemo hakkin al’ummarsa wanda shi a baya ya yi yana dan majalisar tarayya kuma a gaba ma in Allah ya bashi dama.
Abubakar Nuhu danburan ya kara da cewa yanada burin yaga an tabbatarda dokar ilimi kyauta a Nijeriya tun daga furamare har sakandire yakamata ace al’ummar kasa suna samu n ilimi kyauta, da yin tsare-tsare na mutane su sami aikin yi in dalibi ya gama makaranta ba abinyi shike jawo irin abubuwa da ke faruwa na rashin zaman lafiya saboda mutane da yawa ba abin yi mutum kuma sai ya rayu saboda haka zai iya shiga hanya mara kyau damin ya rayu wannan shi ne ba’aso yakamata a fito da tsare-tsare da dokoki da zasu ba mutane na Kano dama saboda in Kano ta saitu Arewa ta saitu.
Ya ce Kano ta tsakiya nada tasirin da duk Wanda zai kasuwanci daga sassan kasarnan da makotan kasashe nan yake zuwa domin gabatar da harkar kasuwanci wannan shi ne abubuwa daya kamata a tsaya akai.
Kuma shi babban burinsa ya tsaya ya kare martabar addini Wanda ya yi hakan a baya a gaba in dama tazo zai yi.
Source: Leadership