Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan shekara na maulidin Annabi Muhammad (SAW)
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da na kasashen waje murnar zagayowar bikin na bana.
Tunji-Ojo, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatare na ma’aikatar, Dakta Oluwatoyin Akinlade, a ranar Litinin din da ta gabata, ya gargadi ‘yan Nijeriya, musamman matasa da su kasance cikin ruhin soyayya, hakuri, da juriya don koyi da Annabi Muhammad (SAW) ), ya kara da cewa, yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya, tsaro da hadin kai a tsakanin al’ummomi a kasar.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi dabi’ar aiki tukuru da neman zaman lafiya ga abokan zamansu, ba tare da la’akari da banbancin addini, akida, zamantakewa da kabilanci ba, sannan kuma su hada kai da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a kokarinta na samar da ci gaba da kasa wacce kowa ke kwadayi kuma duk ‘yan kasa za su yi alfahari da ita.
Ministan ya taya daukacin musulmi farin cikin yin bukukuwan Maulidin cikin kwanciyar hankali da budi da wadata.
A wani labarin na daban wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hoki da ke babban birnin Kano, ta umarci Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh, da ya koma gida ya shirya zuwa wajen bikon matarsa da ta yi yaji.
Kotun wadda ta bayyana cewar, tunda shi G-Fresh bai saki matarsa ba, akwai bukatar ya yi bikon ta domin cigaba da zaman aurensu.
Lauyar G-Fresh, Barr Fatima Aliyu ta bayyana cewa, har yanzun wanda ta ke karewa na matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba.
Kotun dai ta umurci G-Fresh 25 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba da ya sulhunta da matarsa, Sayyada Sadiya Haruna.
Source: LEADERSHIPHAUSA