Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar 2023 na yawan mutane da gidaje da aka shirya fara yi a ranar 3 ga watan Mayun 2023.
Wannan na zuwa ne bayan wafa ganawa da shugaban ya yi da wasu mambobin majalisar zartaswar kasa, da shugaban hukumar kidaya ta kasa a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.
A zaman, sun jaddada bukatar da ke akwai na yin kidayar jama’a da gidaje tun bayan wadda aka yi shekaru 17 da suka gabata domin tattara bayanai da za a yi amfani da su wajen fitar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ci gaban kasa da kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya.
A wata sanarwar da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar Asabar, Buhari ya yaba da irin tsare-tsaren da aka yi domin gudanar da kidayar ta 2023.
Kazalika, ya jinjina wa hukumar bisa fito da hanyoyi masu kyau da inganci da zai bayar da dama a gudanar da hakikanin kidaya kuma wanda za a amince da shi, musamman ta fuskar fito da na’urorin zamani da za su bayar da dama a gudanar da aikin kidayar bisa inganci.