Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsagerun da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari a jihar Borno Rahoton ya ce, akalla mutane 11 ne suka samu munanan raunuka a yayin harin da aka kai a yankin Bama Bayanan tsaro sun shaida cewa, an kuma kai hari kusa da wani sansanin soja, amma bai yi wani tasiri ba.
Akalla ‘yan gudun hijira 11 galibi mata da kananan yara ne suka samu munanan raunuka a yammacin ranar Alhamis, yayin da wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, suka harba bama-bamai uku a garin Banki.
Garin Banki dai na da iyaka da karamar hukumar Bama a jihar Borno da ke Arew maso gabashin Najeriya, Leadership ta ruwaito.
An tattaro cewa an harba bama-baman ne kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Bankin jihar ta barno, ta bayan garin.
Wasu bayanan sirri da aka samu daga Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, a Maiduguri, ya nuna cewa an sake harba wani bam a kusa da sojojin da ke garin, amma bai i tasiri ba.
A cewarsa: “Bama-baman da suka fashe sun sa mazauna sansanin da dama sun yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.
“Sojoji cikin gaggawa sun tura sojoji don dawo da natuswa yankin, yayin da aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.”
Kaduna: ‘Yan sanda sun hallaka ‘yan bindiga 4, sun cafke wata mata mai safarar makamai A wani labarin, wani rahoton BBC Hausa ya ce, jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun kashe ‘yan bindiga hudu da suka addabi mazauna Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar.
‘Yan sandan sun kuma kwato bindigu kiran AK47 da Ak49 dauke da alburusai masu da wata motar aiki da ‘yan bindigan ke amfani da su wajen gudanar da munanan ayyukan su.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, jami’an hedkwatar runduna ta musamman dake Abuja (STS) tare da ‘Operation Yaki Kaduna’ sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke barna a kan hanyar Saminaka zuwa Jos.