Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bukaci gudanar da bincike dangane da harin da aka kaiwa tawagar sojojin Faransa wanda ya kaiga mutuwar mutane 3.
Tawagar sojojin dake kan hanyar zuwa Mali ta gamu da masu zanga zanga a Tera dake Jamhuriyar Nijar abinda ya kaiga amfani da karfi wajen kashe mutane 3 da kuma jikkata wasu da dama.
Tawagar wadda ta isa Cote d’Ivoire ta ratsa ta cikin Burkina Faso kafin ta shiga Nijar akan hanyar ta na zuwa Gao a tsakiyar kasar Mali, inda rundunar Barkhane ke fafatawa da ‘Yan ta’adda.
Kakakin sojin Faransa Pascal Ianni yace babu sojan kasar koda guda da ya samu rauni, amma kuma direbobi guda 2 dake cikin tawagar sun samu raunuka daga duwatsun da aka jefe su, yayin da aka bata wasu motoci.
Shugaba Bazoum ya kuma jinjinawa Faransa saboda abinda ya kira gudumawar da take bayarwa a Yankin Sahel.
A wani labari na daban hadin gwiwar rundunonin sojin Burkina Faso da Nijar sun sanar da kashe ‘yan ta’adda kimanin 100 a wani farmakin da suka kai kan mayakan masu ikirarin jihadi akan iyakokokin kasashen biyu a tsakanin 25 ga watan Nuwamba zuwa 9 ga watan Disamba.
Sanrwar ta kuma kara da cewar, Sojojin Burkina Faso hudu sun rasa rayukansu a wani harin bam da aka binne a gefen hanya.
Tillaberi dake yankin da ya hada iyakokin Nijar, Burkina Faso da Mali ya dade yana fama da Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda masu ikirarin Jihadi da suka addabi sauran sassan yankin Sahel tun shekara ta 2015.