Wata baturiya da ta auri ‘dan Najeriya daga jihar Enugu ta bayyana bidiyon kanta da irin rayuwar da take yi a Najeriya.
Kyakyawar matar ta nuna kanta tana ayyukan gida kamar wanki da shara kuma tace tana jin dadin zaman ta a kasar nan.
Ta kara da bayyana irin farin cikin da take yi da mijinta yayin da ta sanar da cewa burin ta ya cika tunda ta auri ‘dan Najeriya.
Wata baturiya wacce ta auri dan Najeriya ta bayyana yadda take jin dadin zama da mijin ta dan Najeriya.
Ta wallafa bidiyon kanta tana ayyukan gida a Najeriya tare da wasu matan kauye.
Yayin wallafa bidiyon, tace gaskiya akwai sauki sabo da rayuwar Najeriya saboda tun farko ta saba yin ayyukan gida.
Kamar yadda kyakyawar matar wacce aka yi wa lakabi da sunan mace ta gari, tace tana jin dadin zaman ta a kasar nan.
Ta kara da bayyana cewa mijin ta dan asalin jihar Enugu ne kuma ya kasance miji nagari tun bayan da suka yi aure.
Ta wallafa bidiyon ne ta TikTok a shafi mai suna @realhousewifeofnigeria.
Jama’a sun yi martani @jbforever48 yace: “Ba wai kokarin zolaya ba, meye amfanin share dattin?
Na dade ina son sanin haka.” @gloryjimmy0 tace: “Allah yayi miki albarka matar mu ta Najeriya, ina alfahari dake mace tagari.”
@iammrspacillalove tace: “Ina addu’a Ubangiji ya sanyawa auren ki albarka, nima na janyo mijina zuwa Amurka shekaru 9 da suka gabata kuma muna zaman lafiya. Shekarunmu goma da aure.”
@skayonyon ya tambaya: “Daga wacce kasa kike? Kai tsaye zan tafi kasar ku, wannan babbar albarka ce.”
@musbau55 yace: “Wannan abun birgewa ne ka ga mace haka.
Wacce ke zama a Amurka tana irin wannan.
Ina yi muku addu’a, Allah yasa muku albarka a auren ku.”
A wani labari na daban, Kyawawan hotunan fitacciyar ‘yar siyasa kuma tsohuiwar ‘yar takarar gwamnan jihar Kogi, Natasha Akpoti, yayin da ta haifa yaro namiji sun bayyana. Kamar yadda aka gano, matashiyar ‘yar siyasan ta haifa ‘danta na farko ne a ranar 12 ga watan Yulin 2022 a wani asibiti dake Amurka.