Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a sakon babbar sallar bana, ya ce ba zai taɓa haɗa layi da hutu ba har sai yan Najeriya sun samu zaman lafiya.
Yayin taya Musulmai murnar zuwan Babbar Sallah, Buhari ya ce da kowa na koyi da koyarwan addini da duk matsalolin nan sun zama tarihi.
Ya yi kira da Musulmai su yi amfani da wannan lokacin wajen nuna wa abokan zaman su ana tare.
Shugaban ƙasa, Muhammasu Buhari, ya sake tabbatar wa yan Najeriya cewa ba zai huta ba har sai sun samu nutsuwa daga gare shi duba da kalubalen tsaro da tsadar rayuwa da suka dabaibaye ƙasar nan.
Shugaban kasan ya bayar da wannan tabbacin ne a cikin sakon sa na barka da Sallah ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da yan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
“Ina sane da wahalhalun da mutane ke fama da su kuma ina kokarin shawo kan su baki ɗaya,” inji Buhari a wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar. Babbar Sallah: Ba zan huta ba har sai Yan Najeriya sun samu kwanciyar hankali, Buhari.
Shugaban ƙasa, wanda ya yi kira da fifita gina ƙasa, ya bukaci mazauna da su sanya kishin ƙasa a gaba fiye da abubuwan da ran su ke so, kana su yi, “amfani da addini a matsayin kwarin guiwar nuna soyaya ga mutane.”
Buhari ya ƙara da cewa, “idan muka sanya koyarwan addinan mu a aikace, duk waɗan nan sheɗancin da ke hana ruwa gudu sun zama tarihi.”
A cewar mutum lamba ɗaya a Najeriya, “Bai kamata muna amfani da addini a matsayin hanyar banbance juna ba, amma mu ɗauke shi a hanyar yin nagarta ga ƙasar mu da al’ummar mu.”
Sakon taya murnar zuwan babbar Sallah Shugaban ƙasa Buhari ya taya ɗaukacin al’ummar Musulman Najeriya da na duniya baki ɗaya murnar zagayowar sallar layya wato Babbar Sallah 2022.
Ya taya murna ta musamman ga, “Mazan fama maza da mata da ke fagen yaƙi da ta’addanci ta kowane fanni da iyalansu, da kuma waɗan da yan ta’adda marasa imani ke tsare da ku nesa da iyalansu.”
Bugu da ƙari ya yi amfani da wannan lokacin wajen rokon Musulmau su yi koyi da darussan idin layya. inda ya ƙara da cewa: “Ya kamata mu nuna wa abokan zaman mu soyayya da kulawa yayin da muke shagalin wannan lokaci mai muhimmanci a rayuwar mu.”
A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya faɗi wanda Bola Tinubu ya amince zai zaɓa a matsayin mataimaki na gaske Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana wanda Tinubu ya amince zai zaɓa a mataimaki.