Babachir David Lawal ya yi kaca-kaca da Asiwaju Bola Tinubu a kan dauko abokin takara Musulmi.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyan ya ce bai dace a rasa Kirista a tikitin zama shugaban kasa ba Lawal bai goyon bayan Kashim Shettima saboda APC za ta yi takarar Musulmi da Musulmi a zaben 2023.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya nuna bai goyon bayan Musulmi da Musulmi su tsaya takara a jam’iyyar APC.
Daily Trust ta rahoto Injiniya Babachir David Lawal a ranar Talata, 12 ga watan Yuli 2022, yana cewa bai amince da tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima ba.
Allah-wadai da neman takaran ‘dan siyasar a APC:
A wani jawabi da ya fitar a daren yau, tsohon SGF din ya yi kira ga Muhammadu Buhari a matsayinsa na shugaban kasa, ya rusa takarar Kashim Shettima.
“Na yi tunani zan gujewa magana a game da kataborar da babban aboki na, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen zaben abokin takararsa.
Ni ne mutum na karshe da zan yi wa Tinubu adawar zama shugaban kasa. Dalili kuwa tun a 2011 nake matukar goyon bayan ya gaji Buhari.”
Punch ta rahoto Lawal yana mai cewa bai gamsu a tsaida Musulmi da Musulmi su yi takarar shugaban kasa da mataimaki ba, ya ce hakan yana da hadari. Tun ba yau ba, Injiniya Lawal ya bayyana cewa ya fadawa Tinubu illar kin daukar Kirista.
Tinubu ya canza yanzu:
A cewar Lawal, Tinubu mutumin kirki ne, mai daukar shawara, faram-faram da kuma saukin kai, amma ya ce yanzu wasu ‘yan kanzagi sun fara canza shi.
“Za su yi masa karya, su bata sunan wasu, su yi duk abin da za su iya domin neman alfarma, kuma su jawowa na kusa da shi bakin jini, haka aka yi masa.”
Babachir David Lawal Babachir Lawal ya soki Shetima da cewa mai kudi ne wanda yake da dogon buri. A dalilin zaben shi, kiristoci za su yi wa APC bore, a cewar ‘dan siyasar.
Abin ya yi yawa – Lawal Ba zai yiwu ‘dan takara ya fito daga Legas, mataimakinsa daga Borno, shugaban APC na kasa daga Nasarawa, mataimakinsa daga Borno a cewar Lawal ba.
Baya ga haka, shugaban kasa ya fito daga jihar Katsina, ga shugabannin majalisar dattawa na wakilai da mataimakinsa daga jihohin Yobe, Legas da Filato.
Source:hausalegitng