‘Aure sama da 1,500 ya mutu a yankin Yamai na Nijar a 2022’
Ƙungiyar Ƙoli kan harkokin addinin Musulunci ta ƙasar Nijar ta ce duba wayan salalu da wasu dabi’un sun yi sanadin kashe daruruwan aure a ƙasar.
Sai dai ƙungiyar ta ce yawan mace-macen auren ya ragu idan aka kwatanta da shekarar 2021 inda aure sama da 3,000 ya mutu.
Ƙungiyar ta ce ga alama faɗakarwar da malamai ke yi wa ma’aurata, ta yi tasiri wajen samun raguwar mace-macen auren.
Babbar kungiyar addini ta IEN da saba fitar da irin wannan rahoton a kowace shekara.
Cikin rahoton na bana, kungiyar ta ce an sami raguwar mutuwar aure, musamman wanda ita kungiyar ke shiga tsakani a kashe.
Ustaz Mouha na kungiyar ya shaida wa BBC cewa sasantawar da kungiyar ke yi ma’aurata ta hanyar yi musu nasiha ta taimaka wajen rage yawan mace-macen aure a kasar.
“A wannan shekara ta 2022, aure dubu guda da rabi ne ya mutu, inda a baya muka ga dubban mace-macen. Allah ya sa abin ya zo da sauki kwarai.”
Ustaz din ya bayyana manyan dalilan da ke janyo mutuwar aure a Nijar:
“Babban dalili shi ne rashin hakuri tsakanion bangaren macen da na mijin. Akwai kuma wasu abubuwan da iyayenmu basu da su a da, misali salula.”
Ya kara da cewa “Duk macen da ke daukar salular maigidanta tana bincike, ko shi mijin yana daukan na matarsa yana bincike, zai iya ganin wani abin da ba shi da kyau wanda ba zai iya jimrewa ba. Ita ma ba za ta iya jimre ma abin ba.”
Ya kuma ce akwai karya daga bangaren maza, wanda suke yi wa mata gabanin aurensu, inda daga baya sai matsala ta kunno kai bayan matan sun gane an yaudare su ne.
Madam Ahmad Maryama Musa ta wata kungiyar kare hakkin mata da yara, su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan mutanen Nijar game da illolin kashe aure.
“Taron kara wa juna sani da muka shirya ya taimaka, domin malamai da sarakuna da kuma sauran jama’ar gari duka sun halarta. Ta kai ga sun rika tafiya zuwa yankunan karkara domin bayyana wa al’umarsu illar mutuwar aure.”
Kungiyoyin biyu sun ce ba za su tsaya a inda ake ba, domin sun lashi takobin ci gaba da wayar da al’umomin kasar ta Nijar kan illolin mutuwar aure.