Real Madrid na son Harry Kane, Arsenal na nazari kan Hazard
Real Madrid na son sayen Harry Kane don kaka ta gaba. Kwantirgin dan gaban na Ingila na yanzu a Tottenham zai kare ne a 2024, kuma ana ganin farashinsa zai iya kaiwa yuro miliyan 100 kwatankwacin fam miliyan 88.3m. (Todofichajes)
Poland ta tuntubi tsohon kociyan Rangers da Aston Villa Steven Gerrard ko yana sha’awar zama sabon kociyan kasar. (Polish publication Meczyki, daga Mail)
Arsenal na duba yuwuwar zawarcin Eden Hazard, wanda ya yi ritaya daga buga wa kasarsa Belgium wasa a watan Disamba. (Mediafoot)
Chelsea ta bi sahun Tottenham a zawarcin dan bayan Sifaniya Pedro Porro a watan nan sai dai ita ma ta gamu da tarnakin da Tottenham ta gamu da shin na cewa kungiyarsa Sporting Lisbon na son duk kungiyar da za ta saye shi ta biya kudin sharadin katse kwantiraginsa yuro miliyan 45 lakadan. (90 Min)
Besiktas ta amince ta karbi fam miliyan 2.7 daga Manchester United ta bar dan gaban Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 30, ya kawo karshen zaman aron da yake yi a Burnleyda wuri domin ya koma Old Trafford har zuwa karshen kakar nan. To amma kuma kungiyar ta Turkiyya tana son sai ta samu wanda zai maye gurbinsa kafin ta bari ya tafi. (Guardian)
Evertonare na tattaunawa da Villarrealkan karbar aron tsohon dan wasan tsakiya na Bournemouth Arnaut Danjuma, mai shekara 25. (Bruno Alemany)
Ita ma Nottingham Forest na sha’awar dan wasan na Holland, Danjuma. (Sky Sports)
Atletico Madrid are na kallon dan gaban Barcelona Memphis Depay, na Holland a matsayin daga cikin wadanda za ta nema domin maye gurbin, Joao Felix, na Portugal wanda zai tafi Chelseaaro zuwa karshen kakar nan. (sportitalia.com)
Daukan Felix ba zai hana Chelsea neman dan gaban RB Leipzig Christopher Nkunku, ba. Da bazara ne dan wasan na Faransa zai koma wajen Bluesdin. (Fabrizio Romano)
Newcastle United sun mika bukatarsa ta neman dan gaban Jamus Youssoufa Moukoko, wanda Chelsea, ma ke son, kuma za ta iya samun matashin mai shekara 18 idan kwantiraginsa yak are daBorussia Dortmund a bazara. (Evening Standard)
Wata kungiyar Premier da ba a bayyana ba na zawarcin dan wasan tsakiya na Marseille da Faransa Matteo Guendouzi. (L’Equipe )
Dan wasan tsakiya na Holland Teun Koopmeiners,ya ce abu ne da zai dace ya ganshi a Liverpool amma kuma hankalinsa gaba daya na kan Atalanta” kuma yana farin cikin taka leda a kungiyar ta Serie A. (Goal)
Wolves ta sake nuna sha’awarta a kan dan bayan West Ham Craig Dawson, wanda kwantirginsa da Hammers din zai kare a bazara. A bazarar da ta wuce ne kungiyar ta yi kokarin sayen dn bayan na Ingila amma ba ta yi nasara ba. (Express da Star)
Bournemouth are na tattaunawa domin sayen matashin dan wasan gaba na gefe na Burkina Faso Dango Ouattara daga Lorient. (Athletic)