Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kara tsawaita yajin aikin da take da karin wasu makonni hudu domin baiwa gwamnatin tarayya karin lokaci domin biyan bukatun ta.
Kungiyar ta ASUU ta dauki wannan matakin ne a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa a sakatariyar ta ta kasa da ke Abuja ranar Lahadi, The Nation ta ruwaito.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya fitar, kungiyar ta ce: “Bayan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen cika alkawuranta wajen magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2020 (MOA), NEC ta yanke shawarar kare wa’adin yajin aikin zuwa wasu makonni hudu domin baiwa gwamnati karin lokaci don gamsuwa da warware dukkan batutuwan da suka rage.
“Yajin aikin zai fara aiki ne daga karfe 12:01 na safe a ranar Litinin, 1 ga Agusta, 2022.”
A wani labarin na daban gwamnatin afirka ta kudu zata rage farashin man fetur.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Ministan Makamashi da Albarktun kasar, Gwede Mantashe, a ranar Asabar.
Ya ce manufar ragin shi ne saukakawa masu amfani da makamashin samunsa cikin sauki.
Mantasha ya ce gwamnati ta dauki matakin ne duba da yadda ake samun karancin masu sayen man fetur a kasar sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ta tsinci kanta a ciki tun bayan bankewar cutar Korona.
Idan za a iya tunawa a watan Yuni, 2022 ne kasar Afirka ta Kudu ta fuskanta na matsanancin hauhawar farashi kayayyaki da ba ta taba gani ba wanda ya kai adadin 7.4 a shekaru 13 da suka gabata.
Kasashe da dama a duniya na fuskantar matsin tattalin arziki, inda a kasashen Afrika ake samun hauhawar farashi na kayan masarufi, inda wasu kasashen aka fara matsa wa gwamnatoci lamba.
Source 1:hausalegitng
Source 2: Leadershiphausa