Jarumin wasan Hausa Ali Nuhu ya magantu a kan sabon bidiyo da ya bayyana na yan ta’adda suna zane fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ke hannun su.
Ali Nuhu ya kalubalanci gwamnati a kan cewa yanzu haka za ta zuba ido tana kallo ba za ta cika alkawaran da ta dauka na kare al’umma ba.
Sarkin Kannywood ya roki Allah Ubangiji da ya kawowa al’ummarsa mafita a kan wannan hali da suke ciki.
Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya yi martani a kan sabon bidiyon da yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna suka saki.
A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da sarkin Kannywood ya nuna bacin ransa a kan yadda gwamnati ta zuba ido tana kallon yan ta’adda na cin karensu babu babbaka a kasar.
Daraktan fina-finan ya tambaya ko haka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta ci gaba da zuba ido ana azabtar da al’ummanta ba tare da cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka da dukiyoyin talaka ba.
Hakazalika jarumin ya tambayi ina imanin shugabanni da ke rike da madafun iko, inda ya jaddada cewa hakkin al’umma a kansu ba karya bane.
Daga karshe Ali ya roki Allah madaukakin sarki a kan ya kawowa bayinsa mafira a kan wannan hali da suka tsinci kansu.
Ya rubuta a shafin nasa: “Yanzu haka Gwamnatin zata zuba ido tana kallon al’umma da ta yi alkawarin kare rayu kansu da dukiyoyin su a cikin wannan hali? Ina imanin shugabanni? Hakkin al’umma akan ku fa ba karya bane.
“Allah ya kawo hanyar da mutanen nan zasu samu mafita, amin.”
A wani labarin na daban Mun kawo a baya cewa yan makonni bayan farmakin da aka kaiwa ayarin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina, yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya.
An dai farmaki tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabannin bikin Sallah. Mutane biyu sun jikkata a harin wanda aka ce fadar shugaban kasar ta dakile.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, a cikin sabon bidiyon da suka saki, yan bindigar wadanda suka sace fiye da fasinjoji 60 a jirgin kasar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kuma halaka Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Source:hausalegitng