Hukumar INEC ta fitar da jerin wadanda za su shiga zaben Gwamnan jihar Akwa Ibom a 2023.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takaran Gwamna a jihar a zaben badi Jam’iyyar ta samu kanta ne a cikin wasu rigingimun cikin gida da ya shafi zaben fitar da gwani.
Jam’iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya ba ta da ‘dan takarar kujerar Gwamna daga jihar Akwa Ibom a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa daga cikin jerin ‘yan takaran da hukumar INEC ta fitar a Akwa Ibom, ba a ga sunan wanda zai tsayawa APC takara ba.
A karshen makon jiya aka saki sunayen ‘yan takaran gwamnan, aka tabbatar da cewa ba a tsaida wanda zai rikewa APC tuta a jihar Akwa Ibom ba.
Akan Udofia ya fice daga APC Akan Udofia shi ne ake ikirarin ya lashe zaben zama ‘dan takaran APC a jihar, amma hukumar INEC tace ba ta san da zaben fitar da gwanin da aka yi ba.
Kwamishinan zabe na Akwa Ibom, Mike Igini ya gabatarwa INEC rahoto a ranar 27 ga watan Mayu, yana sanar da cewa APC ba ta tsaida ‘dan takara ba.
Har zuwa yanzu matsayin hukumar zaben shi ne ba ta gudanar da zaben fitar da gwani a jam’iyyar APC ba, abin da hakan ke nufi shi ne ta rasa takara.
Rikicin APC na cikin gida a jihar ya jawo jami’an INEC suka kai har karfe 10:30 na dare a filin Sheergrace Arena a ranar, amma ba a fara zaben gwani ba.
Bassey Albert ya bar PDP Kwanakin baya an ji labari Sanata Bassey Albert, ya fice daga jam’iyyar PDP a Akwa Ibom.
Daga baya Albert ya bada sanarwar komawarsa jam’iyyar YPP.
Guguwar sauya sheka ta sake shiga majalisar dattawan Najeriya, Sanatan wanda ya yi shekara bakwai yana Kwamishina Akwa Ibom ya hakura da PDP.
Source:legithausang