Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abubuwa guda takwas da gwamnatinsa za ta fi bai wa fifiko wajen bunkasa tattalin arziki da zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ministan Kudi kuma ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya gabatar da tsarin taswirar tattalin arziki, wanda aka yi la’akari da shi a farkon babban taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya gudana a wannan mako.
Ranar Litinin Za A Kaddamar Da Jirgin Kasan Legas Da Zai Rika Jigilar Fasinja 175,000
Sin Na Shirin Sabunta Dabarun Kare Mabambantan Halittu Na Kasa Da Tsare-tsare
Edun wanda ya bayyana wa manema labarai na gidan gwamnati ajandar da suka hada da samar da abinci, kawo karshen talauci, bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi, damar samun babban jari, inganta tsaro, inganta filin wasan da mutane da kamfanoni za su yi aiki, inganta tsarin dokokin kasa, da yaki da cin hanci da rashawa.
Ya ce majalisar zartarwa ta yi nazari a kan abubuwa takwas da suka fi ba da fifiko tare da gano abubuwan da za a cimma a cikin shekaru uku masu zuwa.
Edun ya ce shugaban kasa ya bai wa ministoci umurnin kan su fitar da manufofi da shirye-shirye a cikin makonni don inganta tattalin arzikin kasa tare da kyautata al’amura ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Edun ya ce majalisar ta amince da cewa tattalin arzikin bai kai inda ya kamata ba.
Game da batun alkiblar majalisar zantarwar ta dosa kuwa, ministan ya ce, “Tun da farko Shugaba Tinubu ya taya kowa murna tare da jaddada babban abin da ‘yan Nijeriya suke bukata, sannan ya karfafa muna gwiwa wajen jajircewa da kuma gudanar da yin aiki cikin gaggawa wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya. Tun da farko, mun gudanar da wani atisaye na duba inda al’amura suka tsaya dangane da tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki, hauhawar farashin kudadin waje, rashin aikin yi da sauransu.
“Babban abin da ya dace shi ne, ba inda ya kamata mu kasance ba, mun kuma yi nazari a kan batutuwa takwas da shugaban kasa zai mayar da hankali a kansu, wato abubuwa takwas da za mu saka a gaba wajen ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba wadanda suka hada da samar da abinci, kawo karshen talauci, bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi, samun jari, musamman wajen samar da bashi, hada kai ta kowane fanni, musamman matasa da mata, inganta tsaro, inganta wuraren zuba jari, bin doka da oda da kuma
Yaki da cin hanci da rashawa.Wannan shi ne ainihin abin da tattaunawar ta kasance.”
Edun ya ce gwamnatin Tinubu ta gamu da mummunan yanayin tattalin arziki tare da hauhawar farashin kayayyaki na kashi 24 cikin 100 da kuma matsanancin rashin.
Tun da farko a wajen kaddamar da taron majalisar zartarwar, Tinubu ya hori ministocin da su duba girman mukamin da ofisoshinsu tare da mayar da hankali kan ayyukan da ke gabansu domin kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar nan.
Source: LEADERSHIPHAUSA