A Yau Ne Ake Gudanar Da Bukin Salla Karama A Najeriya Da ma Wasu Kasashen Musulmi.
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Anatolia ya fitar ya nuna cewa Ayau litinin ne kasashen musulmi 17 ciki harda Najeriya suke gudanar da shagulgulan sallar karama bayan kammala Azumin watan Ramadan mai Alfarma, kasashen sun hada da Saudiyya Qatar baharain, Kuwait, hadaddiyar daular laraba, falasdine,yamen masar Labaon libiya tunusiya iraki Aljeriya da kuma murteniya.
Yayin da wasu kasashen kamar Jamhuriyar musulunci ta Iran jodan Moroko Oman tsibin kanari zasu yi bukin salla karama ne a gobe Talata in mai duka ya kaimu saboda rashin ganin jinjirin watan Shawwal a wadannan kasashen.
READ MORE : Hamas Ta Jinjinawa Jagora Kan Tallafin Da Take Samu Daga Kasar Iran.
Shugaban kwamitin masana limin kimiya dake kula da ganin wata a ofishin jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah Imam Khamna’I sun sanar da gobe talata a matsayin ranar karamar sallah a Iran saboda da rashin ganin jinjirin watan shawwal inda za su yi cika Azumi guda 30 ke nan cur a bana.
READ MORE : Sudan; Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Ajiye Bambance-Bambance Tsakaninsu Da Gwamnati.
READ MORE : Kan Kasashen Turai Ya Rabu A Lokacinda Rasha Ta Rufe Fampon Isakar Gas Ga Wasu Kasashe.