A watan Agusta na wannan shekarar mun yi sharhi mai taken ‘Bukatar A Tausaya Wa Talakawa”, mun sake dawo da sharhin ne saboda muhimmancinsa, musamman ganin rahotannin da ke fitowa na shirin karin kudin makaranta da gwamnati ke yi a fadin kasar nan.
Damuwarmu a nan ita ce, in har wannan labari ya zama gaskiya zai kara matsalar da al’umma ke ciki ta matsin tattalin arziki a daidai wannan lokacin da al’amuran rayuwa ke kara ta’azara a kullum.
Muna kira ga gwamnati ta rika sa talaka a zuciya a yayin shiri da kuma gabatar da dukkan al’murranta.
A duk fadin duniya ana samar da gwamnati ce musamman domin ta kula da jin dadin al’umma da kuma tabbatar kare rayuka da dukiyoyinsu. A kan haka dole kowacce gwamnati ta nuna damuwarta a kan jin dadin al’ummarta.
Tausaya wa talakawa a cikin harkokin gwamnati abu ne da ya kamata a fuskanta a matsayin hakki.
Kowanne dan kasa na bukatar ya samu damar gabatar da abin da ya shafe shi daidai da kowa da kuma damar samun nasara a kan abin da ya sa a gaba, ba tare da nuna bambancin tsakanin talaka da mai kudi ba. Idan har an samar da tsare-tsare da suka ba talakawa muhimmanci, gwamnati na nuna cewa, ta tsayu ne don tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin al’umma kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa, sannan hakan na nuna cewa, lallai gwamnati ta dauki rayuwa da mutuncin al’umma da matukar muhimmanci.
Bayanai na nuna cewa, samar da jin dadin al’umma shi ne, gwamnati ta sanya ido tare da tabbatar da jin dadin al’ummarta ta hanyar ba dukkan bangarori hakokinsu ba tare da nuna bambanci ba, tare da raba dukiyar gwamnati ga dukkan bangarori na al’ummar kasa don su ma su san ana yi da su.
A kasa kamar Nijeriya da ke da bambance-bambance a tsakanin talaka da mai kudi da sauransu, ya zama dole gwamnati ta muhimmantar da abubuwan da suka shafi jin dadin al’umma musamman na mutane da ake nuna wa wariya da bambanci a cikin al’umma.
A matsayinmu na gidan jarida, wannan ne hanyar da muke bukatar shugabannin gwamnnati su dauka domin cimma manufar ingantar rayuwar al’umma.
A ra’ayinmu, al’umma na samun ci gaban da ya kamata ne ta hanyar daga masu rauni a cikinta. A kan haka ya zama dole gwamnati a dukkan matakai su samar da manufofin da za su karfafa talakawa ta yadda su ma za su nunfasa, su kuma shiga cikin tsare-tsaren da gwamnati ke fito da su na ci gaban al’umma gaba daya.
Duk da muna sane cewa, wasu kudurorin gwamnati na daukar lokaci kafin su iya tsayuwa da kafafunsu amma kuma yana da muhimmanmci a samar da gwamnatin da za ta tafi tare da talakawa a kuma ba su damar bayar da tasu gudummawar ga bunkasar tattalin arzikin kasa.
A bayyana yake cewa, al’ummar Nijeriya da dama na fuskantar matsanancin talauci, miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fafutukar ganin sun samu abin kaiwa bakin salati. Idan gwamnati ta muhimmantar da al’amarin talaka a cikin tsare-tsarenta to lallai tamkar ta yi nasarar yaki da talauci ne daga tushe, kamar abin da ya shafi rashin aikin yi, rashin samun ilimi mai inganci da cikakken kiwon lafiya da kuma abubuwan da suka shafi jin dadin al’umma gaba daya. Samar wa talakawa tsare-tsaren gwamnati masu muhimmanci zai taimaka wajen kubutar da su daga kangin talauci tare da samar da daidato a cikin al’umma.
A matsayinmu na gidan jarida mun damu kwarai da gaske a kan yadda ake samun tashin-tashina sakamakon rashin adalci da daidato a cikin al’umma. Watsi da bukatun talakwa da kuma rashin sanya su a cikin tsare-tsaren ci gaba na iya takura su, ya sa su cikin damuwa, wanda hakan zai iya zama tushen tayar da hankulan al’umma. Samar wa talakawa hanyoyin sararawa tare da sanya su a cikin tsare-tsaren bunkasar tattalin arzikin kasa, zai sa talakawan su rage kuncin rayuwa, ya sa su rungumi sauran al’umma, kana su kudiri aniyar kare ci gaban da ake samu a cikin al’umma don sun san su ma suna da nasu kason a ciki. Amma abin takaici a nan shi ne, wannan ba shi a cikin tunanin gwamnatin da muke da shi a dukkan matakai a wannan lokacin.
Yana kuma da matukar muhinmmanci a fahimci cewa, duk wani dan’adam yana da baiwar da Allah ya yi masa ba tare da bambancin talaka da mai kudi ba. Idan har gwamnati ta samar wa talakawa ingantaccen ilimi, aikin hannu da kiwon lafiya a cikin sauki, tamkar ta bude wasu kofofi ne da za a samar da al’ummar da za ta bayar da gudummawar bunkasar tattalin arzikin kasa. Zuba jari wajen bunkasa rayuwar talakawa ba wai yana amfanar da mutanen da suka samu tallafin kadai ba ne amma hakan yana tabbatar da ci gaba mai dorewa a bangaren tattalin arazikin kasa gaba daya.
Muna amfani da wannan damar wajen tunatar da gwamnati cewa, ci gaban kasa ba zai samu nasara ba idan har aka yi watsi da bukatun talaka.
In har gwamnati ta samar da tsare-tsaren bai-daya da zai karfafa talakawa, to gwamnati ta hau hanyar samar da kakkarfar al’umma da soyayya wadda amince wa juna zai yi tasiri a tsakaninsu.
Yayin da gwamnati ke samar da sauye-sauye a bangarorin mulki da dama a cikin wata biyu da suka wuce, yanzu ya zama dole ta tabbatar da dukkan bangarorin al’umma sun shiga cikin shirin ba tare da nuna bambanci ba.
A kan haka muke ba gwamnati shawarar cewa, ta samar da tsare-tsaren da za su rage radadin talauci a cikn al’umma, musammnan ganin yadda aka cire tallafin man fetur, ya kuma kamata a gudanar da wannan cikin sauri ba tare da boye-boye ba.
Source LEADERSHIPHAUSA