Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Sanata Kashim Shatima ya bukaci yan Najeriya su dena la’akari da addini kadai wurin zaben shugabanni.
Tsohon gwamnan na Jihar Borno ya ce yan Najeriya sun mayar da hankali kan batun addinin yan takara a yayin da wasu kasashen duniya ke cigaba a bangarorin fasaha da lafiya Shatima ya yi watsi da zargin da wasu ke yi na cewa kasancewarsa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yan takarar APC barazana ce ga wadanda ba musulmi ba a kasar, yana mai cewa gyaran kasa ke gabansu.
Sanata Kashim Shettima, abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya ce su dena takaita tunaninsu kan addini yayin zaben shugabanni, rahoton The Cable.
Zaben Shettima da a matsayin mataimakin Tinubu ya janyo suka daga mutane saboda su biyu musulmi ne.
Da ya ke magana a ranar Juma’a yayin da ya karbi bakuncin tawagar APC karkashin jagorancin Mohammed Hassan, tsohon jakadan Najeriya a Amurka, tsohon gwamnan na Borno ya ce abin da ke gabansa da Tinubu shine sauya kasar.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa Tinubu ba shi da wani niyyar musuluntar da Najeriya.
“Yanzu muna zamani ne na fasaha, a wasu kasashen, mutane suna zancen fasahar nanotechnology, biotechnology da quick data da artificial intelligence, amma muna nan muna magana kan fadar makiyaya da manoma, yan bindiga, garkuwa, yaki da Boko Haram da maganar hadin addini,”
Ya yi watsi da zargin da ake ma Tinubu na musuluntar da kasar yana mai cewa da gaskiya ne da ya fara daga gidansa.
Ya ce Asiwaju Bola Tinubu musulmi ne amma bai tilastawa yayansa addininsa ba, inda ya ce shine gwamna na farko da ya mika makarantun mission ga masu shi kuma yana daukan nauyin mutane daga kowanne bangare.
A bangarensa, Hassan ya fada wa Shettima cewa ya ziyarci shi ne don sanar da shi game da taron jin ra’ayi da ke tafe inda yan takarar APC za su fada wa mutane tsare-tsaren da suke da shi.
APC Ta Zabi Wanda Zai Maye Gurbin Kashim Shettima a Majalisa.
A wani rahoton, Jam’iyyar APC reshen Jihar Borno ta zabi Antoni Janar na Jihar, Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takarar kujerar sanata na Borno Central da a halin yanzu Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ke kai.
Baturen zabe na jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Uba Magari yayin sanar da sakamakon zaben da aka yi a sakatariyar jam’iyyar a Maiduguri a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli ya ce tsohon kwamishinan shariar ya samu kuri’u 459 cikin 480 masu kyau, rahoton The Sun.
Source:hausalegitng