Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin jihar Kano tallafin tireloli na shinkafa 100 da tirela 44 na dawa da kuma tirela na masara guda hudu domin rabawa mabukata.
Sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
Tofa ya kara da cewa, gidauniyar Dangote ta kuma tallafa wa jihar da buhunan shinkafa 120,000 mai nauyin kilo 10.
“Bayan wannan tallafin, gwamnatin jihar Kano ta raba tireloli 145 na hatsi iri daban-daban domin rabawa a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar,” inji shi.
Tofa ya ce, an samu nasarar aiwatar da wannan shiri ne tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar.
A wani labarin daban ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ta ce an raba kayan abinci cikin tirwla 276 ga jihohin Lagos, Ogun da kuma yankin Babban Birnin Tarayya, FCT.
Sadiya ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja, lokacin da ta ke amsa tambayoyi a taron kowace rana domin jin irin ci gaban da gwamnati ta samu wajen yaki da cutar Coronavirus.
Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sanarwar ware kayan abinci, metirik tan 70,000 domin rabawa ga marasa galihu da zimmar a rage musu radadin zaman gida.
A na sa jawabin, Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce an raba tan 6,800 ga Lagos, Ogun da kuma FCT Abuja.
Ya ce ba da dadewa ba za a raba sauran kayan abincin ga jihohi 13 da cutar Coronavirus ta fi yi wa lahani.
A na ta bangaren, Sadiya ta ce har yanzu hukumar ta ba ta karbi kayan abincin gaba daya ba, saboda yawan sa, kuma ba ta da wurin ajiyar sa idan ma ta karba.
“Dalili kenan daga cikin wanda muka rigaya mu ka karba, mu ka debi cikin tirela 276, mu ka raba a jihohi ukun da Shugaban Kasa ya kafa wa dokar hana fita.
“Nan ba da dadewa ba kuma za mu kara karbowa domin raba wa sauran jihohi 13 da za a a raba wa sauran.” Cewar Sadiya.
Ta kara da cewa akwai sauran kayan abincin yanzu haka jibge a cikin rumbuna ajiye ba a kai ga kwasowa a raba ba.
“Saboda ko metirik tan 2000 zai ci cikin tirela 80. Shi ya sa mu ka bar shi ajiye cikin rumbunan ajiyar abinci.”
Batun rabon kudin da za a ci gaba kuwa, ta ce an yi amfani da shugabannin al’umma, kungiyoyi da kungiyoyin matasa da shugabannin addinai wajen tantance wadanda za a raba wa.
DUBA NAN: Dalibai Sun Rasa Rayukan Su A Cinkoson Karbar Taimakon Abinci A Jami’ar Nasarawa
Ta ce za a bi tsarin BVN ne a raba kudaden ga jama’a a wannan karon. Sannan ta ce ana raba kayan abincin ne ga marasa galihu, daidai yadda zai wadace su tsawon watanni biyu kowanen su.