An san Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023 da iya dabaru idan aka zo kan maganar siyasar yanki da na kasa.
Don haka, a shirye-shiryensa na ganin ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023, jagoran jam’iyyar mai mulki na kasa ya tanadi manyan dakarunsa wadanda tuni suka fara yi masa aiki a fadin kasar.
Joe Ibokkwe ya saki jerin sunayen manyan ginshikan Tinubu wadanda za su taimaka wajen lallasa abokan hamayyarsa don ganin cewa ya gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari. 2023: Cikakkun sunayen dakarun Tinubu da za su kawo masa kujerar shugaban kasa.
A bisa ga jerin sunayen da Igbokwe ya wallafa a Facebook a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, gwamnoni, manyan masu fada aji da jiga-jigan jam’iyyar mai mulki na yiwa Tinubu aiki a akalla jihohi 14.
Borno: Ali Modu Sheriff, Kashim Shettima, da Babagana Zulum
Kano: Ganduje, Kwankwaso, Shekarau da Tanko Yakassai
Kaduna: El-Rufai da Uba Sani Ogun: Abiodun, Osoba, Amosun da Gbega Daniel
Ekiti: Gwamna Kayode Fayemi, Adebayo, Fayose, Oni, Bamidele, da Adeyeye
Osun: Gwamna Oyetola, Baba Akande, Aregbesola da Omisore Nasarawa: Gwamna Sule da Al-Makura
Edo: Adams Oshiomole da Ize-Iyamu
Bauchi: Adamu Adamu da Yakubu Dogara Gombe: Inuwa Yahaya da Danjuma Goje
Kwara: AbdulRahman zai yiwa Tinubu aiki
Katsina: Gwamna Aminu Masari, Hadi Sirika, Dikki Radda da Ibrahim Masari
Zamfara: Gwamna Bello Matawalle, Marafa, Yerima, Yari da Shinkafi
Lagos: Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Fashola, Gbajabiamila, Baba Olusi, Prophet Odunmbaku.
Ya kara da cewa Tinubu zai yi nasara wanda a cewarsa wannan ne dalilin da yasa Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) ya ce ya kamata ya yi a hankali.
A wani labari, tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya ce ya sanyawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima albarka.
Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna dauke da sa hannun Cairo Ojougboh, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Ali Modu Sheriff.
Source; Legitnghausa