Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jajirce kan aniyarsa ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka masu kyau duk da barazanar hukuncin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar.
Gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 3 domin biyan kudin wasu ayyuka a jihar.
Kwamishinan yada Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a wata hira da manema labarai, ya yi nuni da cewa, sam hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ba ta karya musu guiwa ba, duk da cewa, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin rashin adalci, amma gwamnatinsu ta kudiri aniyar ci gaba da gudanar da manyan ayyukan da ta tsara a jihar.
Wasu daga cikin wadannan manyan ayyuka da za a ci gaba, akwai shirin aurar da Mata zaurawa sama da 1000 da shirin bayar da tallafin karatu na daliban jami’ar Bayero ta Kano (BUK) na sama da Naira miliyan 712 da kuma biyan kudin jarrabawar kammala sakandire (SSCE) na sama da Naira miliyan 524.
A cewarsa, za kuma a biya bashin wasu kudaden kwangila har Naira Miliyan 747.8 da ba a biya ba na kwangilar shekarar 2011 zuwa 2015.
Source: LEADERSHIPHAUSA