A ranar Litinin, 1 ga watan Augusta, ‘yan asalin Owu da masu nadin sarauta a jihar Ogun sun karba sabon Olowu na Owu, Saka Matemilola, kuma basaraken ya ziyarci Obasanjo har gida.
Sabon basaraken farfesa ne wanda ya samu darewa kujerar sarautar sakamakon gadon da yayi kaka sa kakanni.
Abun sha’awa shine yadda tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya karba basaraken kuma ya durkusa wurin gaishesa.
A ranar Litinin, 1 ga watan Augustan 2022, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya karba bakuncin Saka Matemilola Adelola, sabon Olowu na Owu, a gidansa dake Abeokuta na jihar Ogun.
Obasanjo, wanda shi ke da sarautar Balogun din Owu, ya karba sabon basaraken tare da ‘yan Owu da kuma masu nadin sarauta a gidansa na Ita-Eko dake karamar hukumar Abeokuta ta arewa. Girmamawa: Obasanjo ya gana da sabon basarake, ya durkusa masa don gaida shi.
Kamar yadda TheCable ta rahoto, tsohon shugaban kasan ya durkusa a gaban Olowu domin yi mishi maraba da zuwa.
A Kasar Daga gidan Obasanjo, an jagoranci sabon basaraken zuwa fadar Adedotun Gbadebo, Alake na Egbaland, domin mika gaisuwa inda daga nan aka kai shi Oke-Ago Owu domin fara shirin nadin sarautar, Premium Times ta rahoto.
Obasanjo ya yabi matasa da gwamnatin jihar Obasanjo ya mika godiya ga duk wanda ke da hannu wurin zaben.
Ya godewa gwamnatin jihar da ta amince da Metemilola a matsayin sabon Olowu kuma ya tabbatar da cewa sabon basaraken zai samu goyon bayan jama’a tare da mulki cikin kwanciyar hankali.
Matsin Rayuwa: Farashin Litar Kalanzir ya kai N800, Ƴan Najeriya sun Shiga Halin Ha’u’la’i.
A wani labari na daban, farashin kalanzir wanda iyalai da yawa ke amfani da shi, yayi tashin gwauron zabi zuwa N800 matsayin kudin lita daya saboda yadda kasuwar ke kokarin juyawa tare da daidaitawa zuwa sabon karin farashin man fetur da iskar gas.
Source:hausalegitng