Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke masarautu 5 da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙira.
Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan.
A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya ce majalisar ta soke dukkan “masarautu biyar da aka ƙirƙira inda za a koma tsarin Masarauta guda ɗaya kamar yadda yake tun zamanin Shehu Usmanu Ɗanfodio, don haka yanzu Kano ta zama da Sarki guda ɗaya idan gwamna ya sanya hannu.”
Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye.
A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar.
Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano.
Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya.
A wancan lokacin, gwamnati ta yi iƙirarin cewa ta ƙirƙiro masarautun ne domin samar da ci gaba a faɗin jihar.
Sai dai a jawabinsa, mataimakin shugaban majalisar dokokin Muhammad Bello Butu Butu ya ce babu wani ci gaba da aka samu bayan ƙirƙirar masarautun.
“An gaya mana cewa idan aka kafa masarautun nan za a samar da sabbin birane da ci gaba a yankunan karkara, don hana hijira daga ƙauyuka zuwa birnin Kano. Amma ku shaida ne cewa ba mu samu wani ci gaban a zo a gani ba sakamakon ƙirƙirar masarautun nan,” in ji shi.
Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na ɗaruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta.
DUBA NAN: Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yiwa Dokar Masarautun Kano Gyaran Fuska
Amma mutanen yankunan da aka ƙirƙiro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ƙara kawo musu ci gaba da bunƙasa.