Assalamu alaikum. Malam ina cikin wani tashin hankali, iyaye na ne suka samo min aiki, mijina ya ce ba zan yi ba, na yi na yi ya ki ya yarda, su kuma sun ce sai na yi, mahaifina ya ce idan mijin nawa ya ki yarda na yi tahowa ta na amshi posting letter na, in mijin ya gaji ya biyo ni.
Dan Allah malam me ye abin da ya kamata na yi, na rasa yadda zan yi? Magana ta gaskiya mijina bai rage ni da komai ba, babu abin da ba ya min kawai dai aiki ya ce ba yanzu ba.
Yanzu ni dai ba na son na saba ma iyayena kuma bana so na ki bin umurnin mijina ya zanyi dan Allah?
Wa alaikum assalam. Ki yi kokari wajan gamsar da iyayenki, da hakurkurtar da su, Idan ba su yarda ba, ki yi biyayya ga mijinki saboda ya fi mahaifinki girman hakki a kanki.
Allah ya yi umarni da biyayya ga iyaye a ayoyi masu tarin yawa a cikin Al’kur’ani da hadisai, saidai a wajan Mace miji yana gaba da Uba, Annabi (SAW) yana cewa: “Inda zan umarci wani ya yi sujjada ga wani, to da na umarci mace ta yi sujjada ga mijinta”.
Tun da mijinki yana biya miki dukkan bukatunki, barin aikin ya zama wajibi, saboda aikin Gwamnati ga mace yana halatta ne in akwai bukata kuma ya aminta daga cakuduwa da maza.
Tafiya wajan aiki ba tare da iznin mijinki ba sabon Allah ne da keta alfarmar Shari’a, Allah ya umarci Mace da ta zauna a gidanta a aya ta (33) a suratul Ahzaab.
Allah ne mafi sani.