Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban abin da zai bar wa ‘yayansa shi ne ilimi, domin ba zai bar musu komai ba a matsayin gado.
Buhari, ya yi wannan jawabi ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar a yau lokacin da ya je gaisuwar sallah masarautar Daura, a jihar Katsina.
“An daure ni sama da shekara uku bayan na shugaban ci kasar nan, a wannan lokacin na gane sannan na gaya wa ‘ya’yana ribar da za su samu shi ne abin da yake cikin kwakwalwarsu, ba abin da suka samu a duniya ba” in ji Buhari
Ya ci gaba da cewa “Abin da nasa a gaba shi ne horar da yara su kasance masu amfani a duk inda suka tsinci kansu. Na gaya wa ‘ya’yana musamman mata cewa zanbyi musu aure ne kawai idan suka kammala digiri na farko”
“Sun san cewa babu abinda zan bari a matsayin gado, babban abin da zan bari shi ne in tabbatar sun samu ingantaccen ilimi” a cewar Buhari
Sannan shugaban kasar ya kalubalanci matasa su tashi su nemi ilimi, kuma ba domin aikin gwamanti ba saboda babu aiki a yanzu, sai domin su horar da kawunansu da koyon wani abun sannan su yi kokarin yakar talauci domin a tafi kafada da kafada dasu a wannan karni na 21.
Source:Leadership