Gwamnatin jihar Kano ta umarci majalisar masarautar Bichi da ta dakatar da bikin nadin sarautar Salisu Ado Bayero a matsayin hakimi a masarautar.
Wata wasika da aka aike wa sakataren masarautar Bichi mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi, Ibrahim Kabara, a madadin mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam, wanda shi ne kwamishinan ma’aikatar, ta ce, ya kamata a dakatar da bikin nadin saboda “wasu bukatun gaggawa” a halin yanzu.
“Dangane da wasikar da kuka aiko mai dauke da lamba Bichi/EM/Adm/018/Vol III/167 mai dauke da taken bikin nadin sarauta mai kwanan wata 2 ga Fabrairu 2024. An umurce ni da in isar da umarnin gwamnati na dakatar da bikin saboda wata bukatar gaggawa a halin yanzu,” in ji wasikar.
Sai dai gwamnatin jihar ba ta bayar da cikakken bayani kan “bukatar gaggawa” a cikin wasikar ba.
A ranar 15 ga watan Fabrairu, 2024, Majalisar Masarautar Bichi ta rubuta wa Salisu Ado Bayero, wani dan uwan Sarkin Bichi, inda ta sanar da shi amincewar Sarkin na nadinsa a matsayin Hakimi a masarautar Bichi.
Duba Nan: Kaddamar Da Sabuwar Hukumar Kula Da Aikin Haji
Wasikar ta umurci Salisu Ado Bayero da ya zo fadar a ranar Juma’a 1 ga watan Maris, 2024, domin yi masa rawani a matsayin Hakimin gundumar.