Karbala (IQNA) Gwamnan Karbala ya sanar da cewa, za a dauki mataki mai tsanani ga mutanen da suke da niyyar cin mutuncin birnin da kuma sunan addini na Karbala, sannan ya ba da umarnin tattara bishiyar Kirsimeti a fadin lardin daga jiya Juma’a.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Barratha cewa, shugaban kwamitin kolin tsaro kuma gwamnan Karbala Nasif al-Khattabi ya jaddada cewa, za a dauki tsauraran matakai don tunkarar mutanen da suke da niyyar cin mutuncin birnin Karbala.
An cire itatuwan kirsemiti da aka gani a titunan birnin na Karbala a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekara tare da kawar da wadannan bishiyun daga titunan birnin na Karbala.
A wani labarin na daban Malamai da mahardata na kasashe 12 ne suka halarci gasar kur’ani da Itrat ta bana, wadda cibiyar Darul Qur’an ta Imam Ali (AS) ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban wannan cibiya Muhammad Ansari ya bayyana cewa: Masu da’awar sun kai 362 daga kasashen waje da suka hada da Afghanistan, Pakistan, Tajikistan, Iraq, Azarbaijan, India, Nigeria, Lebanon, Tanzania, Ukraine, Spain, Syria.
Jagoran ya gabatar da jawabi a wajen rufe gasar karo na 17 da aka gudanar a ranar Juma’a a hubbaren Sayyida Abdul Azim Hosni (AS) da ke birnin Ray da ke kudancin birnin Tehran.
Ya ce: A cikin wannan lokaci kimanin masu fafutukar kur’ani 9,000 ne suka fafata a fagagen karatun kur’ani, haddar (mataki daban-daban), tilawa da fahimtar kur’ani.
Wannan jami’in ya bayyana cewa: Kimanin masana kur’ani 72 ne suka tantance kwazon wadanda suka fafata a bangarori daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa masu shirya gasar suna shirin bullo da sabbin sauye-sauye a wannan gasa da za a fara aiwatarwa a shekara mai zuwa.
Source: IQNAHAUSA