Al’ummar garin Tudun Biri da iftila’in harin bam na sojoji ya afkawa a makon da ya gabata yayin da suke gudanar da Maulidin Annabi (SAW), sun kai karar Gwamnatin Tarayya gaban kotu, inda suka nemi a biya diyyar Naira Biliyan 33 a kan rayukan da aka kashe na mutum fiye da 100.
Al’ummar garin sun kai karar ne ta hannun Alhaji Dalhatu Salihu bisa wakilcin lauyansu, Barista Mukhtar Usman, a ranar 8 ga watan Disamba, 2023 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.
Har ila yau, al’ummar garin na neman gwamnati ta nemi afuwarsu a rubuce tare da wallafawa a manyan jaridun kasar nan guda uku.
A cewar masu karar, sun dauki matakin shari’a a kan gwamnati ne domin tabbatar da kare hakkim wadanda suka tsira da kuma wadanda suka rasa danginsu a harin.
A cikin karar, lauyansu ya ce wadanda aka kashe a harin an take musu ‘yancin rayuwa kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da kuma dokar ‘yancin dan Adam ta Afirka ta shekarar 2010.
Haka nan an shigar da rundunar sojin Nijeriya a cikin jerin wadanda ake ƙara.
Sai dai ba a sanya ranar fara sauraren karar ba, zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Source: LEADERSHIPHAUSA