Kungiyar Jam’iyyatu Ansariddeen Attijjaniyya ta lissafa wasu abubuwa guda biyar da take neman gwamnatin tarayya ta aiwatar bisa kisan kiyashi da jirgin sojojin Nijeriya ya yi wa masu bikin maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.
Kungiyar ta bayyana abubuwan ne a wani taron ‘yan jarida da ta kira a shalkwatarta da ke Abuja.
Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Kaduna
Kotu Ta Yi Wa Mutane 4 Daurin Rai Da Rai Bisa Samun Su Da Laifin Daukar Nauyin Boko Haram
Cikina abubuwan da kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta yi sun hada da gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa kan tare da sabunta bayanai ga al’umma, saboda tabbatar da adalci.
Haka kuma kungiyar ta ce dole ne a karfafa ka’idojin aiki a tsakanin sojojin Nijeriya, musamman ma na tura jiragen marasa matuKi.
Har ila yau, kungiyar ta bukaci a horar da sojoji sanin ‘yancin Dan’adam da kuma kare rayukan fararen hula tare da jaddada tausayawa da mutunta bambance-bambance da kuma fahimtar al’adu, wanda hakan na iya taimakawa wajen hana sake afkuwan wannan lamari.
Ta kuma yi kira da a samar da hadin kan a tsakanin sojoji da kuma al’umma.
Daga karshe, kungiyar ta nemi gwamnatin tartayya ta biya diyyar rayukan da aka salwantar ga iyalan wadanda lamarin ya shafa. Ta ce dole ne a tallafa wa rayuwar iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu da kudade, domin sake rayuwarsu.
Da yake karin bayani, Babban Sakataren Kungiyar na Kasa, Alhaji Alkasim Yahaya ya bayyana cewa, “Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari. Babu wata magana da za ta iya rage radadin da suke ciki, amma za mu ci gaba da yin addu’o’i a gare ku.
“Muna bakin cikin yadda wannan musiba ta faru a daidai lokacin da al’umma ke bikin murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) cikin lumana. Muna kira da rundunar sojin Nijeriya ta gudanar da sahihin bincike kan lamari tare da daukan mataki ga duk wadanda aka samu da hannnu a ciki.
“A matsayinmu na kungiya, muna bukata a nuna gaskiya da rikon amana wajen hukunta wadanda suka aikata wannan kisan kiyashi. Mun san cewa babu wanda ya fi karfin doka, dole ne a hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa ga mabiyanmu ba tare da la’akari da matsayinsu ba,” in ji shi.
Kungiyar ta ce aikata wannan mummunan lamari ba karamin laifi ba ne na take hakkin Dan’adam, musamman a lokacin bikin zagayowar haihuwar Annabi (SAW) da masoya ‘yan Tijjaniyya ke yi duk shekara. Sannan kuma ta yi kira da rundunar sojin Nijeriya da gwamnatin tarayya da su gaggauta daukar mataki cikin gaggawa tare yin amfani da wadannan sharudda.
Ta ce a shirye take ta ba da goyon baya da hadin kai ga masu ruwa da tsaki domin kawo sauyi mai ma’ana da kwanciyar hankali a Nijeriya.
Source: LEADERSHIPHAUSA